An karrama fitattun fina-finai daban daban a bikin “Golden Panda” da ya gudana jiya Asabar a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kasar Sin. A bana, an gudanar da bikin ne a karo na biyu, wanda kuma gungun sassan bunkasa harkokin adabi da al’adu da gwamnatin lardin Sichuan suka dauki nauyin shirya shi.
Bikin na bana, ya hallara baki daga sassan duniya da dama, an kuma gabatar da lambobin yabo ga fina-finai da wasannin kwaikwayo karkashin rukunoni 27. Cikin fina-finan da aka karrama akwai Ne Zha 2, wanda ya lashe lambar yabo ta wasan zane mai motsi mafi kayatarwa. Sai fim din “There’s Still Tomorrow”, wanda ya zama fim mafi kayatarwa. Fim din “She and Her Girls” ya samu yabo na wasan kwaikwayo talabijin mafi ban sha’awa. Sai kuma “A New Kind of Wilderness”, fim mai kunshe da bayanan gaskiya da ya samu lambar yabo ta Documentary mafi kayatarwa. An kuma karrama kafar CGTN da lambar yabo, ta gudummawar musamman a fannin sadarwa a matakin kasa da kasa.
Mashiryansa sun ce bikin “Golden Panda” na bana, ya hallara fina-finai masu takara har 5,343 daga kasashe da yankunan duniya 126, wanda hakan ke nuni ga matukar karbuwarsa a matakin kasa da kasa.
Ana gudanar da bikin ne a lardin Sichuan duk bayan shekaru biyu, kuma manufarsa ita ce karrama shirye-shiryen fim da suka yi fice, tare da yaukaka musayar al’adu. Kazalika, dandali ne na bunkasa fahimtar juna tsakanin mabambantan wayewar kai, da yayata musayar dabi’un dukkanin al’ummun duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp