Talatar nan ne shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya karrama takwaransa na kasar Sin Xi Jinping da lambar yabo ta Afirka ta Kudu.
Da yake jawabi a wajen bikin, Xi ya ce, dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu ta shiga muhimmin lokaci, yayin da amincewa da juna ta fuskar siyasa ke ci gaba da zurfafa, kuma hadin gwiwar moriyar juna a aikace a fannoni daban-daban ta haifar da sakamako mai gamsarwa.
Ya kara da cewa, kasashen biyu sun ci gaba da yin hadin gwiwa a harkoki na kasa da kasa, wanda ya taimaka wajen ci gaba da ma farfadowarsu, tare da ba da gagarumar gudummawa wajen kiyaye moriyar kasashe masu tasowa.
Ya kuma bayyana cewa, zai martaba wannan karramawa, wadda ke nuna alakar abokantaka a tsakanin al’ummomin kasashen biyu, Xi ya kuma yi alkawarin kara himmantuwa wajen ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu.
Sannan a yammacin yau Talatar nan ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa suka gana da manema labaru bayan shawarwarin da suka yi a fadar shugaban Afirka ta Kudu da ke birnin Pretoria.
Xi ya bayyana cewa, a bana aka cika shekaru 25 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu. Dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu ta samu ci gaba mai zurfi a cikin shekaru 25 da suka gabata, inda amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare ya kai wani sabon matsayi.
Haka kuma dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Kudu ta zarce alakar sassan biyu, har ma ta yi tasiri a duniya. Dazun nan shugaba Ramaphosa da Xi sun yi shawarwari a tsakaninsu, inda suka yi musayar ra’ayoyi dangane da ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen 2 a sabon zamani da kuma al’amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya wadanda suka jawo hankalinsu duka, tare da cimma daidaito mai muhimmanci.
A nasa bangaren, shugaba Ramaphosa ya ce, dukkan shugabannin 2 sun amince da zurfafa hadin gwiwar kasashen 2 a fannonin ciniki da zuba jari, da fadada hadin kan moriyar juna a fannonin ababen more rayuwar jama’a, yawon bude ido, ba da ilmi, tattalin arziki na zamani da dai sauransu, tare da kara taimakawa juna a manyan al’amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya. (Ibrahim Yaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp