Da sanyin safiyar Juma’a, ‘yan Boko Haram sun kai hari makarantar Faudiya, wata makarantar Shi’a da ke Gaidam, Jihar Yobe, inda suka kashe dalibai uku kuma suka jikkata wani.
Maharan sun shiga makarantar yayin da daliban ke tsaka da barci.
- Har Yanzu Ba A Kammala Kwangilar Dakin Karatu Da Aka Bayar Shekara 18 Ba
- Bunkasar Da Kawancen Kasuwancin Sin Da Afirka Ke Yi Ta Nuna Gaba Za Ta Fi Kyau
Sun fara harbi ba kakkautawa kafin daga bisani kashe daliban makaranar.
Rundunar ‘Yansandan Jihar Yobe da kuma Ƙungiyar Shi’a ta Nijeriya (IMN), sun tabbatar da kai harin.
Sai dai harin ya jefa mazauna garin cikin yanayin fargaba da rudani.
An gano sunayen daliban da aka kashe: Muhammadu Saleh mai shekaru 22, Ahmed Abdulrahm mai shekaru 21, da Abdullahi Adamu mai shekaru 21.
Maharan sun jikkata Sani Haruna mai shekaru 25 wanda yanzu haka yake jinya a wani asibiti.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp