Akalla mutane 15 ne aka bindige har lahira a unguwar Orlando ta Gabas da ke garin Soweto a Afirka ta Kudu.
Wani rahoto ya nuna cewar wasu mutane da dama na cikin mawuyacin hali a asibiti bayan harin.
- 2023: Tinubu Ya Amince Zai Dauki Musulmi A Matsayin Mataimakinsa
- Abin Da Yasa Ba Mu Buga Sunan Lawan Da Akpabio Ba – INEC
Shaidun gani da ido sun ce maharan sun shiga mashayar ne da sanyin safiyar yau Lahadi, inda suka fara harbe-harbe a kan wasu matasa kafin daga bisani suka gudu a cikin wata farar karamar mota bas.
Rundunar ‘yan sandan yankin ta ce har yanzu ba ta gano dalilin kai harin ba.
Elias Mawela, shugaban ‘yan sanda na lardin Gauteng, ya bayyana lamarin a matsayin “harin abun takaici a kan ma’aikatan da ba su ji ba gani ba.”
Ya kara da cewa maharan na dauke da bindigu da harsashi kirar 9mm a lokacin da suka shiga mashayar.
“Bincike na farko ya nuna cewa mutanen suna jin dadin kansu a cikin gidan ruwa,” in ji shugaban ‘yan sanda.
“Sai kawai suka shigo suka harbe su. Kwatsam, sai suka ji karar harbe-harbe, a lokacin ne mutane suka yi kokarin fita daga mashayar. Ba mu da cikakkun bayanai a halin yanzu na dalilin da ya sa suka kashe wadannan mutane. Za ka ga an yi amfani da babbar bindiga ba kakkautawa. Kuna iya ganin cewa kowane dayan wadannan mutanen yana cikin firgici.
“Yawan harsashin da aka samu a wurin ya nuna gungun mutane ne suka harbe mutanen.”
A wani harin da aka kai a wata mashaya dake lardin KwaZulu-Natal da ke kudu maso gabashin kasar, an kashe wasu mutane hudu.
Har yanzu dai ‘yan sandan ba su damke wadanda suka kai harin ba.