‘Yan bindiga sun kai hari wasu kauyukan a yankin karamar hukumar Bokkos, da ke Jihar Filato, inda suka kashe mutane biyar.Â
Harin ya faru a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, duk da matakan tsaro da hukumomi suka sanya a yankin.
- Dole Ne A Tauna Tsakuwa Don Aya Ta Ji Tsoro
- Magoya Baya Sun Kori Kwankwaso Daga NNPP, Sun Kona Jar Hula A Jihar Neja
An kashe samari guda hudu da wani tsoho a kauyen Rafut.
Wannan harin shi ne na baya-bayan nan a jerin hare-haren da ake kai wa yankin, inda mutane da dama suka rasa rayukansu a wasu kauyuka a farkon watan Oktoba.
Wadanda suka mutu sun hada da mutane biyar a Wumat a ranar 7 ga watan Oktoba, mutane hudu a Kuba a ranar 10 ga watan Oktoba, da wasu a cikin ‘yan makonnin da suka gabata.
Shugabannin yankin sun yaba wa jami’an tsaro saboda daukin da suka kai, amma sun bayyana takaicinsu kan yadda harin ya faru duk da cewa mazauna yankin sun kai rahoton ganin wasu da ba su yarda da su ba.
Sun bukaci hadin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma don hana aukuwar irin wannan a gaba.