Hukumar da ke kula da gidajen yari ta Nijeriya (NCoS), ta ce wani jami’in hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya (NSCDC), ya mutu a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari gidan yarin Kuje da ke Abuja a daren ranar Talata.
Kakakin Hukumar NCoS, Umar Abubakar ne, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Laraba.
- Yanzu-yanzu: Abba Kyari Bai Bace Daga Gidan Yari Kuje Ba, Cewar Hukuma
- Zargin Badakalar Kudade: ICPC Ta Cafke Dan Kwangilar Kotun Koli Na Bogi
A cewarsa, an kuma kashe fursunoni hudu a harin da ya dauki tsawon sa’o’i.
Ya ce maharan da suka yi amfani da ababen sun shiga ta babbar kofar shiga da kuma katangar ginin, sun kuma jikkata wasu jami’an hukumar uku.
“Jimillar fursunoni 879 ne suka tsere daga gidan yarin a lokacin da aka kai harin.
“Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, an sake cafke 443, fursunoni 551 na tsare a halin yanzu, fursunoni 443 sun tsare, fursunoni 4 sun mutu, fursunoni 16 kuma sun samu raunuka, inda ake kula da su a halin yanzu.
“Duk da haka, ana ci gaba da kokarin cafke duk fursunonin da suka gudu,” in ji Abubakar.
Ya ce ya zuwa lokacin da aka kai harin a gidan yarin na Kuje, jami’an soji 38 ne a kasa baya ga jami’an ‘yan sandan Nijeriya, Civil Defence da na DSS.
Ya kuma tabbatar da cewa DCP Abba Kyari da sauran manyan jami’an tsaro da ake tsare da su a gidan yarin ba su tsere ba, inda ya ce “A halin yanzu suna hannu, ba su tsere ba”.
Yayin da yake bayyana cewa an kashe wasu daga cikin maharan yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga, Abubakar ya yi kira ga “asibitoci da sauran cibiyoyin kiwon lafiya da likitoci da su kai rahoton duk wanda ya zo musu domin jinyar raunin harbin bindiga ga jami’an tsaro mafi kusa.”