Mutum 13 sun rasa rayukansu a wasu sabbin hare-hare da aka kai ƙauyukan Rachas da Rawuru da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato.
Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Stephen Gyang Pwajok, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa hare-haren da suka faru da daddare a ranar Talata “ba su da wani dalili kuma abin takaici ne.”
- Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan
- Kotu Ta Ɗaure Mai Horas Da ‘Yan Wasa Shekaru 8 Sakamakon Zargin Luwaɗi Da Ƙaramin Yaro A Kano
Yayin jana’izar da aka yi wa waɗanda suka rasu, ya yi Allah-wadai da harin tare da tabbatar da cewa gwamnati tana ƙoƙarin kawo zaman lafiya a yankin.
Hakazalika, Hakimin Heipang, Da Paul Tadi-Tok, ya buƙaci gwamnati ta hana makiyaya kiwo a yankunan da ba a nan suke a zaune ba, domin hakan zai taimaka wajen rage rikice-rikice da hana masu kai hari.
Ya kuma nemi a farfaɗo da rundunar tsaro ta jihar wato Operation Rainbow, domin ta riƙa kai ɗauki cikin gaggawa idan an samu matsala a ƙauyuka.
Mai bai wa Gwamnan Filato shawara kan harkar tsaro, Janar Shippi Goshwe (mai ritaya), ya tabbatar da cewa gwamnati tana ɗaukar sabbin ma’aikata ƙarƙashin Operation Rainbow domin inganta tsaron al’umma.
Shugaban Ƙungiyar Matasan Berom (BYM), Barista Solomon Nwantiri, ya yi Allah-wadai da kisan tare da tambayar dalilin da ya sa ake amfani da zargin satar shanu a matsayin hujjar kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba.
Waɗannan hare-haren sun ƙara jaddada buƙatar ɗaukar matakin gaggawa da adalci domin kawo ƙarshen kashe-kashe a ƙauyukan Jihar Filato.