Akalla mutane uku ne suka mutu a karamar hukumar Wukari ta Jihar Taraba sakamakon rikicin kabilanci da ya faru tsakanin kabilun Jukun da Tiv, inda wasu da dama suka jikkata kuma yanzu haka suke asibiti.
Iliyasu Mai Riga na daya daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya, bayan da aka kai musu hari.
- Yau Za A Yi Jana’izar Tsohon Wazirin Kano, Sheikh Nasir Muhammad Nasir
- Gwamnoni Sun Mara Wa Matakin Tinubu Na Cire Tallafin Mai Baya
Ya ce wadanda ake zargi cewa ‘yan kabilar Tiv ne suka kai har suka kashe mutane biyu nan take, amma shi ya samu tsira daga bisani ya je asibiti don jinya.
Shi kuwa Zuza Audu Kuta wanda alamarin ya yi sanadiyar kashe masa kani ya ce lamarin ba dadi kam, amma haka Allah ya nufa, saboda haka ya kamata gwamnati ta shigo cikin lamarin domi kawo karshen wanna rikicin kabilanci da ya dade ana fama da shi a fadin Jihar Taraba.
Rumande Inburu shugaban karamar hukumar ta Wukari, ya ce yanzu haka kura ta lafa a rikicin kuma gwamnati na yin duk abin da ya kamata don ganin an kawo karshen wanna tashin hankali na kabilanci da ya addabi yankin na Wukari.
Kakakin rudunar ‘yansandan Jihar Taraba SP Usman Abdullahi Jada, ya ce rudunar ta yi kokarin dakatar da bazuwar rikichin, yanzu haka kuma kwamishinan ‘yan sadan jihar ta Taraba ya ba da umarnin gaggawa da a yi bincike domin gano sanadiyar faruwar rikicin.