An gano gawar Shugaban Jam’iyyar NDC na mazaɓar Fiidi da ke ƙaramar hukumar Makurdi a Jihar Benue, Igbu Job Terhemen.
Rahotanni sun bayyana cewa Terhemen ya bar gidansa ne a daren ranar Talata domin kallon wasan ƙwallon ƙafa a yankin Kanshio.
Bayan da iyalansa suka neme sa suka rasa, sai suka fara bincike lamarin da ya kai ga gano shi da misalin ƙarfe 2 na daren ranar Laraba a sume.
An same shi ne a cikin wani daji kusa da ma’ajiyar man fetur ta NNPC da ke kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo, amma rai ya yi halinsa kafin a kai shi asibiti.
Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun ɗure Terhemen da igiyoyi sannan suka yi masa allurar wani abu da ake zargin guba ce kafin su bar shi a wajen, amma ba su taɓa wayarsa ba.
Sakataren Yaɗa Labarai na NDC a jihar, Agile Bem, ya fitar da sanarwa inda Shugaban Jam’iyyar na Jihar Benue, Mista Ohini Ojegbe, ya bayyana kisan a matsayin “mummunan laifi”.
Jam’iyyar ta yi tir da kisan tare da kiran jami’an tsaro da su gano waɗanda ke da hannu domin fuskantar hukunci.
Sun bayyana mamacin a matsayin jajirtaccen ɗan kishin ƙasa.
Sai sai kakakin rundunar ’yansandan Jihar Benue, DSP Peter Aondongu, ya bayyana cewa rundunar ba ta samu ccikakken rahoto a hukumance game da faruwar lamarin ba.














