Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Nijeriya ta tsallake lokaci mafi tsanani na gyafan tattalin arziƙi, inda a yanzu ƙasar ta shiga matakin shan jar miya.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, 1 ga watan Oktoba, 2026, yayin jawabin da ya yi wa al’ummar ƙasa na bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Nijeriya.
A cikin jawabinsa, shugaban ya kare tsauraran matakan da gwamnatinsa ta ɗauka na cire tallafin man fetur da kuma daidaita darajar Naira, yana mai jaddada cewa waɗannan gyare-gyaren sun zama dole domin ceto tattalin arziƙin ƙasar da ya daɗe yana fuskantar matsaloli.
Hakazalika, shugaban ya gargaɗi ’yan Nijeriya da su guji sauraron kiraye-kirayen dawo da tallafin man fetur gabanin zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa yin hakan zai iya mayar da ƙasar baya tare da rushe nasarorin da aka riga aka samu.
Tinubu ya bayyana cewa tattalin arziƙin Nijeriya ya haɓaka da sama da kashi huɗu cikin 100 (4%) a shekarar 2026.
Ya ƙara da cewa hauhawar farashin kayayyaki ta ragu sosai, ajiyar kuɗaɗen waje ta ƙaru, satar ɗanyen mai ta ragu, sannan kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta daidaita.
A cewarsa ƙasar ta samu sama da dala biliyan shida ($6 billion) ta hanyar fitar da kayayyakin da ba na mai ba zuwa ƙasashen waje a shekarar 2025.
Gwamnatin Tarayya ta lashi takobin cewa za ta karkata akalar ayyukanta wajen inganta rayuwar talakawa ta hanyar ƙara zuba jari a fannonin noma, hanyoyi, layin dogo, wutar lantarki, masana’antu, da kuma sadarwar zamani.
Haka kuma, ya yi alƙawarin ƙaddamar da tsare-tsaren tallafi irin su Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND) da CREDICORP don rage raɗaɗin wahalar rayuwa.
Ko da yake shugaban ya amince tsadar rayuwa ta addabi jama’a, amma ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin rage kuɗaɗen samar da kayayyaki da sufuri.
“Yanzu manufarmu a bayyane ta ke: wadata kowa da kowa,” in ji Tinubu.














