Rundunar sojin Nijeriya ta sallami wasu dakarunta biyu wadanda aka samu da laifin satar wayoyin wutar lantarki a matatar Dangote da ke Jihar Legas.
Wasu jami’ai na kamfanin tsaro mai zaman kansa da kuma wasu sojoji suka kama wadanda ake zargin, Kofur Innocent Joseph da Lance Kofur Jacob Gani bisa laifin sata.
- Yadda Makafi 44 Suka Zana Jarrabawar JAMB A Bauchi
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 A Kasuwa A Zamfara
Wata sanarwa da daraktan yada labarai na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar ranar Litinin, ya ce an samu mutanen biyu da laifin barin wajen aikinsu yayin binciken da aka gudanar.
Nwachukwu ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun gaza yin aikinsu yadda ya kamata da kuma saba wa dokokin aikin soja kamar yadda yake a sashe na 57 ya tanada.
Ya ce bayan kammala bincike ne, rundunar ta dauki matakin sallamar jami’an biyu tare da mika su ga hukumomin da suka dace domin gurfanar da su a gaban kotu.
“Muna sonbganin mun ci gaba da jajircewa a kan aikinmu na kare ‘yan kasa. Muna kira ga al’umma da su ci gaba da ba mu goyon baya a kokarinmu na samar da tsaro da zaman lafiya a kasar nan,” in ji sanarwar.