An kwace kambun Hilda Baci na zama sarauniyar dafa abinci ta duniya bayan da ta shiga gasar dafa abinci mafi tsawo wacce ta shafe kusan awa 100 tana dafe-dafen abinci kala-kala.
Wani mai dafa abinci dan kasar Ireland, Alan Fisher, ne ya doke Hilda Effiong Bassey ‘yar Nijeriya a matsayin wacce ta lashe gasar tseren girki mafi dadewa a duniya, in ji kwamitin Guinness World Records (GWR) a ranar Talata.
- Gargaɗin Amurka Kan Nijeriya Na Tada Hankulan Masu Zuba Jari A Kasar – Minista
- Abarbar Benin Ta Shaida Yadda Kasar Sin Ke Kara Bude Kofarta
Fisher “Ya dafa abinci na tsawon sa’o’i 119 da mintuna 57 na ban mamaki a gidan abincinsa da ke Japan,” in ji GWR, inda ya karya tarihin da Hilda ta kafa a watan Mayu.
Idan ba a manta ba, matashiyar mai shekaru 26 a duniya ta fara dafa abinci a ranar Alhamis 11 ga watan Mayun bana kuma ta ci gaba da dafa abincin har zuwa ranar Litinin 15 ga watan Mayu.
Ta dafa abinci kala daban-daban har na tsawon sa’o’i 100 a cikin kwanaki hudun da ta kwashe tana girki babu kakkautawa.
GWR sun ce Hilda wacce ta yi niyyar kafa tarihin girki na tsawon sa’o’I 100, ta gaza cimma burin nata bayan da aka soke sa’o’I 7 cikin lokacin da ta kwashe tana girki biyo bayan zarcewar lokacin hutun da ya kamata ta dauka a farkon lokacin da ta fara girkin.
GWR sun bayyana cewa, kamar yadda aka tanadarwa duk wanda zai shiga wannan gasa na girki na dogon zango, an amince ya dauki hutun minti biyar cikin kowace sa’a da zai yi yana girkin.
‘Yar Indiya Lata Tondon ce ta samu kambun gasar ta baya a shekara ta 2019 bayan da ta kwashe sa’o’I 87 da minti 45 tana dafa abinci.