Hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) ta sake karbar wasu ‘yan Nijeriya 159 da suka makale a kasar Libya yayin da suke dawowa gida.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba a Legas.
- Majalisa Ta Goyi Bayan CBN Kan Sauya Fasa Fasalin Naira Bayan Tafka Muhawara
- Dakarun Soji A Jihar Kaduna Sun Kara Kashe Wani Jagoran ‘Yan Bindiga Gudau Kachalla
NEMA ta ce da yammacin ranar Talata ne mutanen da suka dawo suka isa filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Ikeja.
Sun iso Nijeriya a cikin jirgin Al Buraq Air Boeing 737-800 mai lamba 5A-DMG.
NEMA ta ce wadanda aka dawo da su sun hada da maza 71 da mata manya 74, da jarirai 14.
Mista Mustapha Ahmed, Darakta-Janar na NEMA, ne ya karbi wadanda suka dawo a madadin gwamnatin tarayya a hukumance, a cewar sanarwar.
Ya shawarce su da su yi koyi da abubuwan da suka faru da su kuma su kasance masu bin doka da oda.
Sanarwar ta ce, Ahmed, ya samu wakilcin Mista Ibrahim Farinloye, Kodinetan ofishin hukumar na Legas.
Ya ce Gwamnatin Tarayya ta jajirce wajen ganin ‘yan Nijeriya ba su makale a kasashen ketare ba.