• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Nada Ibrahim Rilwan A Matsayin Sabon Garkuwan Matasan Arewa

bySulaiman and Shehu Yahaya
1 year ago
Arewa

LABARAI MASU NASABA

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

Kungiyar Dalibban Nijeriya da hadin gwiwar kungiyar Matasan Arewa sun karrama Malam Ibrahim Rilwan Mohammed (Shugaban Gidauniyar IRM) a Matsayin Garkuwan Matasan Arewa.

Taron Wanda ya gudana a dakin taro na gidan Tarihi ( Arewa House) da ke Kaduna, kungiyar ta bukaci masu Hannu da shuni da su rika taimakawa marasa galihu a cikin al’umma.

  • Harin Gwoza: Gwamnonin Arewa Sun Bukaci Dakile ‘Yan Ta’adda Duk Inda Suke
  • Lamunin Naira Biliyan 5 Ga ‘Yan Fim: Yaushe Kannywood Za Ta Samu Nata?

A jawabinsa Mataimakin Shugaban Majalisar dalibban Nijeriya ( NANS) Kwamared Kabiru Aminu ya bayyana cewa an zabi wanda za a karramawar ne saboda dimbin gudumuwarsa ga ci gaban dalibban da kuma matasan Nijeriya a kowanne mataki. Bugu da kari ya bayyana namijin kokarin wanda aka karrama wajen sha’anin kyautata rayuwar mata da matasa ta hanyar sana’o’in hannu domin su kasance masu dogaro ga kawunan su a cikin garuruwan su, yana mai cewa irin kyakkyawar rawar da gidauniyar sa take takawa wajen daukaka Kalmar Allah ta hanyar ginin Masallatan Jumma’a da na Hamsar Sallawati da kuma Makarantun Islamiyya a birane da karkara a kowanne yankin dake cikin kasarnan da kuma Nijar.
Ya bayyana Malam Ibrahim Rilwan Mohammed a matsayin mai tsoron Allah da gudun duniya kari ga karimcinsa musamman ga marasa galihu.

A nasa jawabin Shugaban kungiyar Matasan Arewa (Arewa Youth Forum for Liberty) Abdulmalik Zakari ya bayyana cewa kungiyar tayi bincike mai zurfi wajen tantace mutane masu kokari da dawainiyar mutane ba tare da gajiyawa ba.
Ya kara da cewa samun irinsa ya yi wuya a yankin Arewa balle kuma a kasar bakidaya. Ya bayyana cewa Lambar Yabon da Sarautar Garkuwan Matasan Arewa za su karfafa masa gwiwa domin ya ci gaba da aiwatar da ayyukan alheri domin wasu su yi koyi dashi.
A cikin jawabinsa wani malamin Addinin Musulunci Farfesa Mansur Yalwa ya shawarci sabon Garkuwan Matasan Arewa da ya ci gaba da gudanar da ayyukan alheri domin Allah ba domin fadanci ba. Ya yabawa wadanda suka shirya taron saboda karrama mutane irin su Malam Ibrahim Rilwan Mohammed da su ke bayar da babbar gudumuwa wajen daukaka Kalmar Allah musamman abinda ya shafi sha’anin Ilimin Addinin Musulunci da Ilimin Zamani a kowanne mataki.
Da yake jawabi Shugaban Gidauniyar IRM kuma sabon Garkuwan Matasan Arewa Malam Ibrahim Rilwan Mohammed ya bayyana godiyarsa ga Kungiyar dalibban Nijeriya da kungiyar Matasan Arewa da suka zabe shi domin bashi Lambar Yabo da Sarautar Garkuwan Matasan Arewa. Ya bayyana cewa a matsayin sa na Musulmi ya yi daidai ya taimakawa mutane saboda yana daya daga cikin koyarwar Musulunci, ya bayyana cewa saboda haka yake taimako saboda Allah.
Ya bayyana cewa a shigo wani lokaci da mutane ba su taimakon makota KO ‘yan uwan su, kuma idan an ga wani na taimakon al’umma sai a danganta haka da cewa yana son wani mukamin siyasa ne. “Ina tabbata maku cewa ba domin siyasa ko son wani mukamin siyasa nake yin wannan taimako ba”.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya
Labarai

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba
Labarai

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci
Labarai

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Next Post
An Fara Kashe Kudi A Firimiyar Ingila

An Fara Kashe Kudi A Firimiyar Ingila

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version