Tun a ranar Litinin ne Cibiyar Ciniki da Masana’antu na yankin babba birnin tarayya Abuja, ta bukaci gwamnatin tarayya da na jihoihi su fito da tsarin biyan haraji na bai-daya a yankuna su domin a samu saukin tafiyar da harkokin kasuwancdi a tsakanin jihohin kasar nan.
Sabon shugaban kungiyar da aka zaba kwananan nan, Cif Emeka Obegolu, SAN, ya yi wannan kiran a sakonsa na murnar bikin kirsimeti ga al’ummar Nijeriya.
- Akidar Siyasar Malam Aminu Kano Da Ta ‘Yan Siyasar Yanzu A Mizani –Farfesa Habu
- Bashin Ilimi Ga Daliban Nijeriya: Manufar Da Ba Ta Da Kyakkyawar Manufa
Ya kuma kara da cewa, duk da cewa, biyan haraji hakki ne da ya rataya a kan dukkan dan kasa, haka kuma harajin na taimaka wa gwamnati wajen sauke nauyinta na gudanar da ayyukan raya kasa ga al’umma kasa.
‘Amma kuma yadda ake dorawa al’umma hadaji kala kala yana darkushe ci gaban kamfanoni da masu zuba jari wanda hakan kuma yana taimakawa wajen mutuwar manya da kananan kamfanoni a sassan kasar nan yana kuma taimawa wajen korar masu zuba jari’ in ji shi..
Masu zuba jari da masu kamfanoni da dama sun sha kokawa a kan yadda ake dora musu haraji barkatai a akan haka suke neman a hada kan dukkan harajin da ake bayarwa ya zama dunkule waje daya don ya rage wa masu harkokin kasuwanci wahahalun da suke fuskanta.
A sanarwar da ya sanyawa hannun da kansa ya kuma nemi gwamnati ta samar da yanayin da zai taimakawa harkokin kasuwanci bunkasa, kamar wutar lanbtarki, tsaro da sauransu kudin da kamfanin ke kashewa sun kai naira Biliyan 1 a duk shekara kuma gashi harkokin kasuwancin ya yi kasa, babu riba.
Wani daya nemu mu sakaya sunansa, ya ce, duk dalilan da kamfanbin ya bayar daidai ne, musamman ganin masu hulda da shagon suna ta kara raguwa ne a cikin shekara 2 da suka wuce, wannnan kuma saboda mastalar tattalin arzkin ne da ake fuskanta a kasar baki daya.
“Manyan masu kudi ne ke zuwa don yin sayayya a shagon kuma ba su zuwa a kai akai, tabbas babu yadda harkar kasuwanci zai tafi a haka.
“Al’umma Kano da dama da ke fama da yadda za su fuskanci rayuwar yau da kullum ba ba za su iya shiga shagon sayen kayyaki masu tsada ba, a kan haka a ka mayar da shagon ya zama wajen zuwa a yi kallo tare da daukar hoto ko kuma a sha ‘ice cream’ (abin da bai wuce naira 1,000 ba), ta yaya zaka biya kudin haya na Naira miliyan 66 kuma har ka ci riba?”
A nasa tsokacin, Sakataren kungiyar masu manyan shaguna a Jihar Kano (National Association of Supermarkets), Umar Habu Ibrahim, ya ce duk da cewa, manyan shaguna da dama sun dakatar da harkokin su a jihar Kano a ‘yan shekarun nan amma dalilan ficewar Shoprite ya sha banban da nasu.
Ya ce, babban dalilin da ya sa Shoprite ya dakatar da harkokinsa sun hada da matsalar tattalin arziki da kuma karyewar darajar Dala da kuma tsadar harkar sufuri. Saboda suna shigo da kusan dukkan kayyakin da suke sayarwa ne daga kasashen waje, a kan haka ya nemi gwamnati ta kawo musu dauki, musamman ganin ficewar irin wannan katafaren kamfanin ba zai harfar wa da tattalin arziki kasa da mai ido ba.