An yi kira ga dukkan al’umma Nijeriya su rungumi akidar yi wa shugabanninmu addu’ar samnun nasarar kai kasar nan tudun muntsira.
Shugaban al’umma Zabarmawa na yankin Agege ta jihar Legas, Alhaji Dauda Abubakar ya yi wannan bayani a tattauanwarsa da manema labarai a ofishinsa da ke Agege a Legas.
- Sabon Kwanturolan NIS Na Jihar Legas Ya Karɓi Ragama
- Bankin TAJ Ya Kafa Sabon Tarihi A Harkokin Bankin Nijeriya
Ya kuma kara da cewa, daga dukkan alamu Shugaba Tinubu yana da shiri na alhairi don bunkasa rayuwa da tattalin arzikin kasar nan, a kan haka kuma ya kamata mu bashi dukkan goyon baya, musamman ta hanyar yi masa addu’ar samun nasara.
Ya kuma yi kira da wadanda za su samu shiga gwamnatin a matsayin ministoci da masu bashi shugaban kasa shawara su sa tsoron Allah da tausayin al’umma a zukatansu ta hanayar aiwatar da manufofi na alhairi da shugaba Tinubu ya kudurta.
Daga karshe ya nemi al’ummar Zabarmawa mazauna yankin Agege dama Jihar Legas gaba daya da su rungumi akidar zama lafiya da saura al’umman da suke zaune da su. Ya ce, sai da zaman lafiya za a iya cimma nasarorin rayuwa. Ya kuma nemi su zama masu bin doka da oda a duk inda suka samu kansu.