Shugaban Hukumar Tashoshin Jirage Ruwan Nijeriya NPA, Mohammed Bello Koko ya sanar da cewa wasu mutane sun sha alwashin bata masa suna tare da yi masa zagon kasa amma kuma ya tsayu a kan ganin bai amince da hakan ya faru ba, ba zai amince da hakan ba.
Ya kuma mkara da cewa, a cikin shgekara 2 da suka wuce, a wani kokarin ganin an yi mani zagon kasa da kuma tashi wasu kudade daga gare ni, wasu mutane ne da ba a san ko su wanene ba ne, suna fakewa da wasu kungiyoyi masu fafutukan kare hakkin bil adam, sun rungumi yi mini zagon kasa ta hanyar amfani da kafafen yada labarai na intanet wajen cimma wannan mummunan buri nasu na yi mini zagon kasa.
- Gwamnan Zamfara Ya Rage Yawan Adadin Ma’aikatun Jihar Daga 28 Zuwa 16
- Tinubu Zai Sanar Da Sabuwar Ranar Kidayar Jama’a Da Gidaje – NPC
Ganin sun kasa cimma mummunan buri sun na bata mini suna da mutunci a halin yanzu sun sake rungumar mummunan shirin ganin sun kawo mani hari ni da da iyalai na.
Saboda sun kasa fitowa fili a gane ko su wanene, na kasa samun daman neman hakki na a kotu a kan karyar da suke yadawa a kai na.
Ina son kara jaddada cewa, a duk shekarun da na yi na aiki a banki da bangaren aikin gwamnati har zuwa yanzu ba a taba samu na da wani laifin aikata ba daidai ba a wani kotu a fadin tarayyar kasar nan. Wannan kuma a bayyana yake ga al’umma gaba daya. Ina kuma da yakinin cewa, mutuncina da aiki tukuru a fagen aikin gwamnati ya sanya Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar daukaka girma na daga Babban Darakta a banagaren harkokin kudi zuwa shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa NPA.
Wasu nasarorin da muka samu sun hada da: Kammala majiyar Bitument mai girman 6,000 don kara girman mattarar Bitumen din da kuma saukaka samar da Bitume din yankin Kudu maso kudu. Samar da mashina 24 don amfani da su wajen sa ido a Shirin na na ‘Truck E-Call Up’ a yankunan Apapa/TCIPC/ da Ijora don rage cunkoson ababen hawa.
Da kuma tabbatar da bin doka amfani da ‘E-Call Up’ wanda hakan ya taimaka wajen samar da tsaro da kuma rage cunkoso a tashashin jiragen ruwa Nijeriya.
Bayar da lasisi ga karin wasu tashoshin akiye motoci don kara inganta ayyukan tashoshin jiiragen ruwa.
Ganin dannan nasarorin da muka samu, b azan yarda wadansu banzaye su shagaltar5 a nib a daga aikin dake gab ana, b azan taba yarda su kawar da hankali na bad aga aikii tukuru da kokarin bunkasa harkokin NPA, wannan shi ne kuduri a yanzu da shekaru masu zuwa a nan gaba.
A karkarewa, ina mai sanar da cewa, daga yanzu zan dauki mataki na shari’a a kan duk wata kafar sadarwar da ta kuskura buga wani bayani a kan na da ya nemi ya bata mani suna ko ci mani mutunci.
Zan kuma yi amfani da al’umma masu mutunci wajen yakar duk wani ma iyi mani zagon kasa da kuma kokarin bata mani suna.
Aiki na a NPA ba na kashin kai na ba ne. Aiki ne na bauta wa kasa, wanna nkuma na sha alwashin gudanarwa dea dukkan kafin na tun a nkaron farko.