An rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin sabon shugaban kasar Senegal na biyar.
Faye mai shekaru 44 ya zama shugaban kasar Senegal mafi karancin shekaru.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane Ana Tsaka Da Sallar Tahajjud A Zamfara
- Isra’ila Ta Kori Kafar Talabijin Ta Al Jazeera Daga Kasarta
Leadership ta ruwaito cewa ya karbi ragamar mulki daga hannun Macky Sall a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu a wani taron da shugabannin Afirka suka halarta a garin Diamniadio, kusa da Dakar babban birnin kasar.
“Al’ummar Senegal su shaida, na yi rantsuwa kuma zan shiga ofishin shugaban kasar Senegal cikin aminci,” in ji Faye.
“Zan yi aiki bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulki da dokoki” da kuma kare “mutunci da ‘yancin kai na kasa, da kuma cimma hadin kan Afirka”.
An gudanar da bikin mika mulki a hukumance daga shugaba mai barin gado Macky Sall a fadar shugaban kasar da ke Dakar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp