Ya zuwa yanzu, an riga an kama kashi 88.3 bisa 100 na yankin bikin baje kolin kasa da kasa na kasar Sin kan ayyukan samar da hidima (CIFTIS) na shekarar 2022, kamar yadda masu shirya bikin suka bayyana.
Mataimakin shugaban ofishin gudanarwa na CIFTIS Zhao Qizhou, ya bayyana cewa, sama da kamfanoni 1,000 da suka hada da kamfanoni 275 cikin kamfanoni 500 dake kan gaba a duniya, da manyan masana’antu ne, suka tabbatar da halartar bikin baje kolin ta yanar gizo da kuma a zahiri. Baya ga kasashe 25 da kungiyoyin kasa da kasa guda 6, da su ma suka sanar da aniyyarsu ta halartar baje kolin.
A cewar Zhou Yiwei, babban manajan rukunin kamfanin nune-nune da ayyuka na Beijing Capital Group Exhibitions & Events, bikin baje kolin na bana, zai gudana ne a filin da ya kai fadin murabba’in mita 152,000, karuwar murabba’in mita 26,000.
Za a gudanar da bikin baje kolin a birnin Beijing ne daga ranar 31 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumba mai zuwa.
Daga cikin abubuwan da za a gudanar, sun hada da taron cinikayyar hidimomi na duniya, da nune-nune, da taruka, da baje sabbin kayayyaki da fasahohin zamani, da tallata harkokin kasuwanci da tattaunawa, da ayyukan tallafawa.
Ana kuma sa ran a karon farko, bikin zai samu sashin hidima a fannin muhalli. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)