Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu dalibai mata su biyar a Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-ma (FUDMA) a Jihar Katsina.
Wata majiya mai tushe a yankin ta tabbatar da sace daliban kuma ta ce an sace su ne a gidansu da ke bayan makarantar Mariamoh Ajiri Memorial International da misalin karfe 2:30 na safiyar Laraba.
- An Gurfanar Da Mutane 14 Kan Karyar Bacewar Mazakuta A Abuja
- Libya Ta Ba Da Umarnin Tsare Jakadiyar Brussels Kan Zargin Cin Hanci Da Rashawa
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da sace daliban, ya kuma ce ‘yansanda sun kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin.
Ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano abubuwan da suka faru da kuma ceto wadanda aka yi garkuwa da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp