Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta kori jami’anta uku wadanda aka samu da laifukan rashin da’a, amfani da bindiga ta hanyar da bai dace ba, cin zarafin aiki, rashin mutunta tsarin aiki da almubazzaranci da harsasai.
‘Yansandan da lamarin ya shafa sun hada da Insifekta Dahiru Shuaibu, Sajent Abdullahi Badamasi, da kuma Sajan Isah Danladi, wadanda ke aikin bai wa fitaccen mawakin APC da ke Kano, Dauda Kahutu Rarara kariya.
- Xi Jinping: Turbar Zamantarwa Ta Kasar Sin Tana Da Manufa, Tsare-tsare Da Dabaru
- Ko Meye Ya Yi Zafi Mane Ya Nushe Sane Bayan Shan Kaye
A ranar Juma’a 7 ga watan Afrilu yayin da suke aikin ba da kariya ga mawakin a kauyensu da ke Kahutu a Jihar Katsina, inda aka hange su suna ta harba harsasai duk da cewa tsarin aikin ‘yansanda ya haramta irin hakan ga kuma fargabar da harbi a kusa da jama’a ciki har da yara a kusa da su.
LEADERSHIP ta labarto cewa Rarara fitaccen mawakin ne da ya yi shura wajen tallata jam’iyyar APC tun 2015 har zuwa zaben baya-bayan nan da aka gudanar.
Jami’in watsa labarai na hukumar ‘yansandan Nijeriya, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya ce abin da ‘yansandan suka yi ba kawai ta’addanci ba ne ko rashin kwarewar aiki, face cin mutuncin aikin ‘yansanda da ma kasa ne baki daya.
Ya ce an dauki matakin ne bayan tkorafe-korafen da suka amsa da aka gano ‘yansandan a wani bidiyon da aka yada a Intanet.
Daga bisani rundunar ‘yansandan ta gargadi dukkanin jami’anta da suke gudanar da ayyukan da ke gabansu bisa tsarin da aka dora su a kai kamar yadda yake tsari a bisa doka domin kaucewa fadawa irin wannan matakin.
Kazalika rundunar ta bukaci jami’an da ke sanya ido da su tabbatar sun ci gaba da bayar da horo ga jami’antq domin tabbatar da’a a kowane lokaci.