Yayin da ake ci gaba da alhinin rasuwar shahararren dan kwallon Brazil da duniya baki daya, Pele, hukumar da ke yi wa jarirai rajista a Kasar Peru, ta ce iyaye 738 ne suka saka wa ya’yan da suka haifa sunan mamacin.
Kamar yadda rajistar da ke dauke da sunayen ta nuna, an rika saka sunayen daban daban kamar Pelé, King Pelé, Edson Arantes, ko kuma Edson Arantes do Nascimento, wanda shi ne cikakken sunan na Pelé.
- Ra’ayin Al’umma: A 2023 Al’ummun Duniya Na Da Imani Kan Gudummawar Sin Ga Bunkasar Ci Gaban Duniya
- Yadda Biranen Sin Suka Farfado Yana Aike Kyakkyawan Sako Ga Duniya
Pelé’ ya mutu ranar Alhamis, bayan ya sha fama da ciwon daji, ya mutu yana da shekaru 82.
Tuni dai Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), ta bukaci kasashen duniya da su ware filin wasa guda daya don sanya sunan Pelé.
An kai gawar Pelé filin wasa na tsohuwar kungiyarsa ta Santos, inda aka ajiye ta na tsawkn awa 24, inda dubban mutane suka dinga zuwa suna yin bankwana da shi.
An birne Pelé da yammacin ranar Talata a birnin na Santos, wanda jana’izar tasa ta samu halartar manyan shugabannin duniya.