Gwamnan Kano, Engr Abba Kabir Yusuf, ya sauya sunayen Makarantar Wasanni da Hukumar Wasanni ta jihar don girmama ƴan wasa 22 da suka mutu bayan gasar wasannin ƙasa a jihar Ogun.
Daga yanzu, za a kira su:
– Makaranta Wasanni ta Ƴan Wasa 22 ta Jihar Kano
– Hukumar Wasanni ta Ƴan Wasa 22 ta Jihar Kano
- Ƙwallon Mata: Rivers United Ta Doke Nasarawa Amazons A Wasan Ƙarshe Na Kofin Shugaban Ƙasa
- Za a Binne Ɗantata A Madina, Za Ai Yi Sallar Ga’ibi A Kano
Sakataren Labarai na Gwamna, Mustapha Muhammad, ya bayyana cewa jihar Kano tana alfahari da sadaukarwar mamatan ƴan wasan.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi Uwargida Oluremi Tinubu wacce ta ba da Naira miliyan 110 ga iyalan marigaya.
An kuma yi alƙawarin cewa gwamnati za ta ɗauki nauyin ilimin yaran waɗanda suka rasu da kuma taimaka wa matansu da iyayensu.