Rundunar Ƴansanda ta Jihar Kano ta sanar da taƙaita zirga-zirga a ƙananan hukumomin Ghari, da Tsanyawa, da Bagwai da Shanono, kafin gudanar da zaɓukan cike gurbi da za a yi ranar Asabar, 16 ga watan Agusta.
A cewar rundunar, wannan mataki zai fara aiki daga tsakar dare na ranar Juma’a, 15 ga watan Agusta, har zuwa ƙarfe 6 na yamma ranar Asabar, 16 ga watan Agusta. Manufar shi ne tabbatar da zaman lafiya da tsaro yayin zaɓen cike gurbi na mazabar Ghari/Tsanyawa da na Bagwai/Shanono.
- Majalisar Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukuma Bisa Zargin Kara Farashin Takin Gwamnati
- APC: Ko Sadaukarwar Ganduje Za Ta Dakile Barazanar Jam’iyyun Adawa A Zaben 2027?
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa, an ware motocin da zasu yi aiyukan gaggawa, irin su motar asibiti, da motar kashe gobara, da motocin da ke ɗaukar ma’aikatan zaɓe, da kuma waɗanda aka tantance a matsayin masu sa ido kan zaɓe.
Haka kuma, an haramta wa waɗanda ba masu kaɗa ƙuri’a ba da kuma wakilan jam’iyyun da ba su da izini zuwa rumfunan zaɓe, tare da hana sanya tambarin jam’iyya da ɗaukar makamai. An kuma hana yawo a kusa da rumfunan zaɓen, kana hukumomin tsaro na jiha irin su ƴan bijilanti da jami’an KAROTA an hana su shiga rumfunan zaɓe.
Kwamishinan ƴansanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa an ɗauki matakan tsaro tare da haɗin gwuiwar sauran hukumomin tsaro. Ya kuma yi alƙawarin cewa jami’an za su kasance masu adalci, ba tare da nuna son kai ba, tare da neman haɗin kan jama’a domin tabbatar da zaɓe cikin lumana da gaskiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp