Wata kotun Majistare da ke zamanta a Ilorin, a ranar Laraba, ta bayar da umarnin tsare mutane 13 da ake zargi da kashe Olukoro na Koro a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara, Oba Segun Aremu, a gidan yari.
An gurfanar da wadanda ake zargin ne da laifin hada baki da kisan kai da garkuwa da mutane da bayar da bayanan karya.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sarki Da Yin Awon Gaba Da Matarsa Da Wasu Mutum 2 A Kwara
- Masu garkuwa Sun Rage Farashin Kuɗin Fansar Matar Sarki Bayan Sun Kashe Sarkin A Kwara
Mutanen su ne, Godwin Jacob, Olowofela Oyebanji da Adefalolu Ayodele da Tewasie Francis da Babatunde Samuel da Godwin Joseph da Issa Number sai kuma Miracle Solomon.
Sauran sun hada da Abraham Kehinde da Muhammed Bello da Muhammed Muhammed da Ahmadu Umaru da kuma, Muhammed Dankai.
Rahoton ‘yan sanda na farko ya bayyana cewa wani mutum mai suna, Aremu Simon Adeyemi ne ya kai rahoton kisan Olukoro zuwa sashin ‘yan sanda na Eruku.
“Wadanda ake zargin sun nuna masa bindiga, inda suka umarce shi da ya bi su a lokacin da ya kalubalance su bayan ya lura da motsin su a kusa da jikansa.
“Ya ce jikan nasa ya tsere ne ta bayan gida, yayin da wadanda ake zargin suka je suka kashe sarkin, suka yi garkuwa da matarsa da wata Mercy,” FIR ta ruwaito Adeyemi na cewa.
Dan sanda mai shigar da kara, Abdullah Sanni, ya sanar da kotun bukatar da ke kunshe da rahoton ‘yan sanda, inda ya bukaci kotun da ta ci gaba da tsare wadanda ake zargin.
A hukuncin da ta yanke, Alkalin Kotun Mai shari’a, Monisola Kamson, ta bayar da umarnin a tsare wadanda ake zargin a gidan gyaran hali na tarayya sannan ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 5 ga Maris, 2024.