Masarautar Bauchi ta tsige Alhaji Muhammadu Bello Kirfi, daga mamba a majalisar bisa abin da ta misalta rashin biyayya da rashin mutunta gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad da aka same shi da yi.
A wasikar tsige Bello Kirfi daga mamban majalisar masarautar ta Bauchi mai dauke da kwanan wata Talata 3 ga watan Janairun 2023 dauke da sa hannun sakataren masarautar, Alhaji Shehu Mudi Muhammad da wakilinmu ya ci karo da ita.
- Kwalara Ta Kashe Mutane 620 A Malawi
- Tashar Jiragen Ruwa Ta Shanghai Ta Kasance Mafi Hada-Hadar Kwantenoni A Duniya A 2022
Wani bari na wasikar na cewa, “An umarce ni da na koma ga wasikar da aka samu daga ma’aikatar kananan hukumomi da ke kula da harkokin masarautun gargajiya mai lamba MLG/LG/S/72/T da ke dauke da kwanan wata 30 ga watan Disamban 2022.”
“Wasikar na kunshe da cewa ba ka biyayya da mutunta mai girma gwamnan Jihar Bauchi da gwamnati kan hakan an umarci a cire ka nan take.
“Bisa bayanan da suke a sama, an cire ka daga ofis a matsayin Wazirin Bauchi kuma mamba a cikin majalisar masarautar Bauchi”.
Alhaji Shehu Mudi Muhammad daga bisani ya yi wa korarren Wazirin Bauchi fatan alkairi a rayuwarsa ta gaba.
LEADERSHIP Hausa ta yi tilawar cewa shi dai Wazirin Bauchi, Alhaji Muhammad Bello Kirfi an taba dakatar da shi daga sarautarsa a zamanin mulki gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar wanda Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu ya yi a watan Maris na 2017.
Bayan da gwamna Bala Muhammad Abdulkadir ya zama gwamna a 2019 ya shiga ya fita har aka samu nasarar sake dawo da shi sarautarsa, yanzu kuma an kore shi gaba daya.