Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Nasarawa, Shetima Jauro-Mohammed, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike kan mutuwar wasu yara biyar a unguwar Agyaragu da ke Ƙaramar Hukumar Obi, ta jihar.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar SP Ramhan Nansel, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce an gano gawarwakin yaran ne a cikin wata tsohuwar mota da aka ajiye a harabar gidan wani mutum mai suna Abu Agyeme.
- Ƴan Ta’adda Sun Kashe Maharba 10 A Adamawa
- Mutum 20,000 Sun Nemi Gurbin Aikin Mutum 4,000 Cikin Kwana Ɗaya A Adamawa
SP Ramhan Nansel, ya ce kwamishinan ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin gano yadda lamarin ya faru da kuma musabbabin mutuwar yaran ‘yan tsakanin shekaru shida zuwa goma.
Yayin da ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan da suka rasa ‘ya’yansu, kwamishinan ya gargaɗi iyaye da masu motoci da su riƙa kula da yadda yara ke mua’amula da motoci, musamman waɗanda suka daɗe a ajiye ko aka bar su babu kulawa.
Saboda yadda jikin yaran da suka rasun ya babbake, Rundunar ‘Yansanda ta tabbatar da cewa tuni ta miƙa gawarwakin ga iyayensu don gudanar da jana’iza kamar yadda suka bukata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp