Sufeton Janar na hukumar ‘yansandan Nijeriya, IGP Usman Baba, ya umarci kwamishinonin ‘yansanda da ke shugabantar Shalkwatar hukumar a jihohi da cewa, dukkanin binciken da suke kan yi na Kesa-kesan da suka shafi karya dokoki da ka’idojin zabe ta shekarar 2022 da aka samu yayin zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu su tabbatar sun kammala su.Â
A cewarsa, bayan sun kuma kammala binciken to su tabbatar sun tura dukkanin fayel-fayel na Kesa-kesan zuwa ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) domin gudanar da su a gaban kuliya mance sabo.
Kazalika, IGP din ya kuma bukaci kwamishinonin da su nemi masu ruwa da tsaki a jihohin domin ganawa da tattauna muhimman batutuwa domin kyautata hidimar tsaro da inganta harkokin zabe.
A cewa Baba, hakan zai taimaka wajen jawo kowa da kowa a jika wajen Bada nasa gudunmawar ta fuskacin inganta tsaro domin tabbatar da an samu gudanar da zaben Gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi a ranar 18 ga Fabrairu cikin kwanciyar hankali, inganci kuma sahihi.
Shugaban na ‘yansandan kasa ya kuma yi kira ga al’ummar kasa da su yi aikin hadin guiwa da hukumar ‘yansandan da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da ingancin tsaro a lokacin zaben.
Ya ce akwai bukatar tabbatar da tsaro ga su kansu masu zaben, masu sa Ido, jami’an INEC, kayan aikin zabe, al’umma da dai sauransu, Kuma ya ce za a cimma hakan ne kawai ta hanyar gudunmawar kowa da kowa.