Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, ya umurci Hukumar Bincike ta Nijeriya (NSIB) da ta fara gudanar da bincike cikin gaggawa kan hadarin jirgin kasan fasinja da wata motar BRT da ke jigilar ma’aikatan gwamnati zuwa wuraren aikinsu a Legas da safiyar Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa, an tabbatar da mutuwar mutane biyu yayin da da dama suka samu raunuka daban-daban a lokacin da jirgin kasan ya yi karo da motar kamfanin BRT a tashar motar PWD da ke unguwar Ikeja a jihar Legas.
Da yake bayyana hatsarin a matsayin abin takaici, Sirika ya baiwa jama’a tabbacin cewa hukumar bincike ta kasa za ta binciko musabbabin faruwar hatsarin za ta kuma samar da hanyoyin da za a bi domin kaucewa afkuwar irin lamarin a nan gaba.
Mataimaki na musamman ga ministan kan harkokin sadarwa, Dr. James Odaudu, ya kuma ce ministan ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Legas musamman wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan ibtila’in, tare da addu’ar Allah ya bawa wadanda suka samu raunuka sauki cikin gaggawa.