A ranar Talata ne wakiliyar musamman ta babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Bintou Keita ta yaba da hadin kan da sojojin wanzar da zaman lafiya na kasar Sin suka nuna wajen gudanar da ayyukan jin kai a yankin gabashin kasar.
Ta yi wadannan kalamai ne a wajen bikin kaddamar da wata gada ta wucin gadi da ta ratsa kogin Luzira a yankin Kalehe na lardin Kivu ta Kudu, yankin da ruwan sama mai karfi da ambaliya a watan Mayu ya yi kamari, wanda ya janyo hasarar rayuka.
Gadar mai muhimmanci ga jigilar kayayyakin jin kai da zirga-zirgar jama’ar yankin, injiniyoyin dakaru na 26 na kasar Sin ne suka gina ta, bisa umarnin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo (MONUSCO).
Yayin da take taya murnar nasarar da aka samu a wannan aikin jin kai, Keita, shugabar kungiyar MONUSCO, ta yaba musamman, da hadin kan da dakarun Sin masu shudin hula suka nuna. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp