Mahukunta a kasar Sin, sun fitar da wani kundi mai kunshe da tsare tsaren bunkasa tattalin arzikin sassa masu zaman kansu, ta hanyar kyautata yanayin gudanar da kasuwanci, da inganta manufofin daka iya tallafawa kudurin, da karfafa tsarin shari’a wanda zai samar da tabbaci ga ci gaban fannin.
Kundin ya bayyana yadda gwamnati za ta taimakawa ci gaba, da kyautata, tare da karfafa tattalin arzikin sassa masu zaman kansu, ta yadda sassan za su taka muhimmiyar rawa wajen ingiza farfadowar kasar ta Sin.
Kaza lika domin samar da kyakkyawan yanayin cimma wannan buri, Sin za ta yi aiki tukuru wajen kawar da shingayen shiga kasuwanni, da aiwatar da cikakkun manufofi, da tsare-tsare na wanzar da takara mai tsafta.
Har ila yau, za a aiwatar da karin manufofi na ingiza samar da kudade ga kamfanoni, da biyan bukatun kwadago masu alaka da manufar.
Bugu da kari, domin bunkasa managarcin ci gaban tattalin arzikin sassa masu zaman kansu, gwamnatin Sin za ta karfafa gwiwar kamfanoni masu zaman kansu wajen gaggauta sauyawa zuwa amfani da na’urorin zamani, da zuba karin jari a fannonin bincike da samar da ci gaba. (Saminu Alhassan)