Tun daga jiya Lahadi ne kasar Sin ta fara aiwatar da manufar dauke haraji kan hajojin dake shiga kasar daga kasashen Afirka masu karancin wadata, dake da huldar diflomasiyya tare da Sin.
Matakin na nufin wadannan kasashe za su ci gajiyar yafiyar haraji dari bisa dari a dukkanin rukunonin hajojinsu masu shiga Sin, inda kasar Sin ta kasance babbar kasa mai tasowa ta farko da ta dauki irin wannan mataki, kuma ta farko cikin kasashe masu karfin tattalin arziki da ta dauki wannan muhimmin kuduri.
- Gwarzuwar Ma’aikaciyar Banki A Shekarar 2024: Dame (Dr.) Adaora Umeoji
- Gwarzon Shekarar 2024: Barr. Nyesom Ezenwo Wike
Da yake tsokaci game da hakan, yayin wata zantawa da manema labarai, sakataren jami’iyyar ZANU PF mai mulki a Zimbabwe Christopher Mutsvangwa, ya ce matakin na Sin shaida ce dake tabbatar da aniyar kasar ta bunkasa bude kasuwanninta, kuma hakan zai ingiza cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka.
Shi ma wani kwararre a fannin alakar kasa da kasa dan kasar Madagascar Rabenja Claudio, ya ce irin hajojin da za su ci gajiyar wannan sauki sun hada da na Madagascar, kamar albarkatun gona, da na masaka da kayayyakin tufafi, da abincin teku da kayayyakin sana’o’in hannu.
Shi kuwa Yang Baorong, mai nazari a cibiyar bincike ta Sin da kasashen Afirka, cewa ya yi baya ga dauke haraji, Sin na duba yiwuwar aiwatar da cikakkun matakai na taimakawa nahiyar Afirka ta fuskar ingiza cinikayya, baya ga ta hanyar kulla yarjejeniyar cinikayya, akwai tallafawa cinikayyar sassan kasa da kasa ta yanar gizo, da taimakawa masu baje hajoji daga kasashen na Afirka, da damar shiga a dama da su a nau’o’in baje koli da ake gudanarwa a kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)