Wata kotun majistare da ke zamanta a unguwar Mai Alluna a jihar Kano ta yanke wa wani matashi hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari bisa samunsa da laifin yunƙurin daɓa wa mahaifinsa Almakashi.
Lamarin ya faru ne a yankin Fagge da ke jihar, biyo bayan wata ‘yar taƙaddama tsakanin wanda ake zargin da mahaifinsa kan kuɗi.
- Boko Haram Sun Kashe Mutum 300 A Sabbin Hare-hare 252 A Borno – Ndume
- EFCC Ta Gurfanar Da Ɗan China A Kotu Kan Bayar Da Bayanan Ƙarya
A cewar ‘yansandan, matashin ya yi yunƙurin kai wa mahaifinsa hari ne bayan yn hana shi kudi da yake son yin amfani da su.
A sakamakon haka, an gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kuliya bisa tuhumarsa kan wannan laifin wanda kuma ya amsa laifin lokacin da aka karanta masa tuhumar.
A hukuncin da ya yanke, Alkalin Kotun, Mai shari’a Nasir Ahmad ya yanke hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, da tarar Naira 20,000, da karin ɗaurin watanni shida a gidan yari, da kuma bulala arba’in.
Kotun ta ce, an yanke wannan hukuncin ne don ya zama izini ga masu shirin aikata irin wannan laifin a nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp