Wata babbar kotun Jihar Osun da ke Ede ta yanke wa wasu mutane biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsu da laifin yin garkuwa da wani bafulatani, Alhaji Ibrahim Adamu.
Waɗanda aka yanke wa hukuncin, da Ibrahim Issa, da Lateef Bello, da Abdul Ramon Soliu, da Bello Ibrahim, da Abudu Mumini Jolaanobi Saheed, an gurfanar da su ne a gaban kuliya bisa zargin haɗa baki da yin garkuwa da mutane da kuma kisan kai.
Amma sun musanta aikata laifin a lokacin da aka gurfanar da su a ranar 28 ga Oktoba, 2021.
- Kotu Ta Rushe Dokar Da Ta Tsige Aminu Ado Bayero A Matsayin Sarkin Kano
- Rikicin Masarautar Kano: Kotu Ta Sake Ɗage Shari’ar Zuwa 4 Ga Watan Yuli
Lauyan da ya shigar da ƙarar Faremi Moses ya gabatar da shaidu yayin shari’ar da ke nuna cewa mutanen biyar sun yi garkuwa da Adamu ne a ranar 17 ga Afrilu, 2018, daga gidansa da ke Owode-Ede, Jihar Osun. An yi garkuwa da Adamu a motarsa kirar Toyota Corolla kuma aka kashe shi bayan iyalansa sun biya kuɗin fansa Naira miliyan uku.
Mai shari’a Kudirat Akano ta samu wadanda ake tuhuma da laifuka guda hudu. Sakamakon haka ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.