Wata babbar kotun Jihar Zamfara ta yanke wa wani Anas Dahiru hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe abokinsa.
Anas da ke Unguwar Dallatu da ke Gusau a Jihar Zamfara, ana zarginsa da kashe abokinsa, Shamsu Ibrahim da wuka kan takaddama kan Naira 100 a shekarar 2017.
- 2024: Majalisar Zartaswar Adamawa Ta Amince Da Kasafin Naira Biliyan 225
- Wang Yi: Sin Da Angola Sun Kafa Misali Na Hadin Gwiwar Kasashe Masu TasowaÂ
Alkalin kotun, Mukhtar Yusha’u, ya ce bayan sauraron bangarorin biyu, kotun ta gamsu cewa Anas ya aikata laifin.
Mai shari’a Yusha’u ya yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya kamar yadda yake a sashe na 221 na kundin laifuffuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp