Wata babbar kotun Jihar Legas da ke zamanta a Ikeja, ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsu da laifin fashi da makami da kuma garkuwa da wata mata Misis Gloria Emole.
Wadanda aka yankewa hukuncin, Ifeanyi Maduaka, Victor Chukwunonso, Obinna Nwankwo, da Richard Nwabueze, an ce sun aikata laifukan ne a ranar 19 ga watan Nuwamba 2012 da misalin karfe 8:30 na safe.
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Zababben Dan Majalisar Dokokin Jihar Benue, Sun Kone Motarsa
- EFCC Ta Shirya Tsab Don Bincikar Gwamnoni 2 Masu Barin Gado Kan Zargin Badakalar Kudade
An gurfanar da su ne a kan tuhume-tuhume guda uku da suka hada da hada baki, fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a ranar 13 ga watan Yulin 2013, wanda Jihar Legas ta fifita su a kai, aka kuma tsare su a gidan yari.
Dokta Babajide Martins, darakta mai shigar da kara na jihar, ya shaida wa kotun cewa sun yi garkuwa da matar da ke shirin barin gidanta da ke lamba 7 a titin Unity a Unguwar Ogudu a Legas.
A cewar mai gabatar da kara, laifukan da aka aikata sun sabawa kuma ana hukunta su a karkashin sashe na 297,285 (2)a da 291 na dokokin laifuka na Jihar Legas na 2015.
“An yi garkuwa da wadda aka abun ya shafa a ranar 19 ga Nuwamba, 2012 kuma an sake ta a ranar 22 ga Nuwamba, 2012, bayan mijinta ya biya kudin fansa Dala 70,000.”
Mai shari’a Lateef Lawal Akapo, a ranar Alhamis, ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun samu damar tabbatar da shari’ar ba tare da wata shakka ba.
Sannan kuma ta yanke wa wadanda ake tuhumar hukuncin daurin shekaru 10 a kan laifin da ake tuhumar su da su na farko.
“An yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda tuhume-tuhume na biyu na fashi da makami, sannan kuma an yanke musu hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari saboda tuhume-tuhume na uku na garkuwa da mutane,” in ji mai shari’a Lateef.