A yau Asabar ne gwamnatin yankin musamman na Macao, ta gudanar da shagalin bikin cika shekaru 26 da dawowar yankin na Macao karkashin jagorancin kasar Sin, inda albarkacin ranar aka gudanar da bikin daga tuta a babban dandalin “Golden Lotus” dake Macao.
Da karfe takwas na safiyar yau din ne dakarun tsaro na bikin, suka raka tutocin Sin da na yankin musamman na Macao zuwa dandalin, yayin da ake busa taken kasa, kana sannu a hankali aka daga tutocin zuwa sama.
Cikin mahalarta bikin, akwai babban kantoman yankin Macao Sam Hou Fai, da daraktan ofishin tuntuba na gwamnatin tsakiyar kasar Sin a Macao Zheng Xinchong, da manyan jami’an gwamnatin Macao, da kuma wakilai daga sassa daban daban na al’umma.
Yayin bikin, wani matashi mazaunin Macao mai suna Huang Tzu Tsai, ya shaidawa kafar CMG ta kasar Sin cewa, zuciyarsa ta cika da farin ciki da mararin ganin dagawar tutocin Sin da Macao a lokaci guda.
Matashin ya ce sama da shekaru 26, tun bayan komawar yankin Macao karkashin kasar Sin, yankin na musamman ya samu yanayin zaman lafiya, da walwala da daidaito, wanda hakan sakamako ne na managarcin goyon baya daga babban yankin Sin. (Saminu Alhassan)














