A yau ne aka yi gwaji karo na 3 na bikin kade-kade da raye-raye na murnar bikin bazara na kasar Sin da CMG ya tsara, inda aka yi bitar gudanar da bikin da ake sa ran watsa shi ta talabijin a ranar 28 ga wata da muke ciki, a dandamalin nuni da aka kafa a biranen Beijing, da Chongqing, da Wuhan, da Lhasa, da Wuxi na kasar a lokaci daya. (Bello Wang)