A yau ne aka gudanar da taron tattaunawa na kungiyar hadin gwiwar kafofin watsa labaru na telebijin na kasashe masu bin shawarar “ziri daya da hanya daya” na shekarar 2023 a birnin Beijing, wanda babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya karbi bakuncin gudanar da taron, inda wakilai fiye da 120 na kafofin watsa labaru 54, daga kasashe da yankuna 33 suka halarci taron ta yanar gizo ko a zahiri.
A cikin jawabin sa, shugaban gidan CMG, kuma shugaban majalisar kungiyar hadin gwiwar kafofin watsa labaru na telebijin na kasashe masu bin shawarar “ziri daya da hanya daya” Shen Haixiong, ya ce shekarar 2023 shekara ce ta cika shekaru 10, da shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”.
Ya ce ya kamata kafofin watsa labaru na kasa da kasa su bi tunanin shawarar, wato yin tattaunawa da raya kasa, da more fasahohin juna, da daukar alhakin dake wuyansu, da raba darajar bai daya ta dan Adam, da taka muhimmiyar rawa wajen yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa, da sa kaimi ga raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’Adama, da yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, don samar da gudummawa ga raya kasa ta wannan fanni. (Zainab)