LAn yi taron tattaunawa kan littafi na 5 na harshen Ingilishi na shugaban kasar Sin Xi Jinping kan dabarun shugabanci mai taken “Xi Jinping: The Governance of China” a birnin Nairobin Kenya a jiya Litinin.
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin da hukumar kula da sadarwa da wallafe-wallafe cikin harsunan waje ta kasar Sin da ofishin jakadancin Sin a Kenya ne suka shirya taron karatun littafin, wanda ya samu mahalarta kimanin 200.
Da yake jawabi a taron, Hassan Omar Hassan, sakatare janar na jam’iyyar United Democratic Alliance ta Kenya, ya ce littafin na 5 ya shimfida tubalin sauya tsarin harkokin zamantakewa da na tattalin arziki a fadin duniya.
Shi kuwa Mo Gaoyi, mataimakin shugaban sashen wayar da kai na kwamitin kolin JKS kuma daraktan ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar, cewa ya yi, dukkan litattafan 5 na shugaba Xi Jinping kan dabarun shugabanci, sun gabatar da wata gaggarumar nasara ta tarihi da hanyar samun ci gaba da kuma sigogin tafarkin zamanatar da kasar Sin. (Mai fassara: FMM)














