An yi tattaunawar kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara: More damarmaki tare da duk duniya”, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG ya shirya, jiya Litinin 10 ga wata, a birnin Chicago dake kasar Amurka. Mataimakin shugaban sashen fadakar da al’umma na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban CMG, Shen Haixiong, da jakadan Sin dake Amurka, Xie Feng, sun gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Karamin jakadan Sin dake Chicago, Wang Baodong, da tsohon gwamnan jihar Illinois, Pat Quinn, da Hon. Lori E. Lightfoot, wadda ta taba rike mukamin magajin garin Chicago, da sauran wasu baki kusan 100 sun halarci bikin, inda suka yi musanyar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi damarmakin da ci gaban kasar Sin mai inganci ya kawo wa duniya, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da hadin-gwiwar tattalin arziki da kasuwanci da sauransu. Daga nan ne kuma, aka kaddamar da jerin tattaunawa ta kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara: More damarmaki tare da duk duniya”.
Za kuma a gudanar da irin wannan tattaunawa a kasashen dake yankunan Turai, da Afirka, da Gabas ta Tsakiya, da Latin Amurka, da kuma Asiya. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp