Wasu mahara dauke da makamai sun kashe manoma biyar a ranar Laraba a kauyen Yelwata da ke karamar hukumar Guma a Jihar Benuwe.
Mazauna kauyen sun shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa, manoman na aiki ne a gonakinsu, inda maharan suka yi musu yankan rago.
- Kwamitin Tsakiya Na Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin Ya Zartas Da Sanarwa Game Da Cikakken Zamansa
- Kotu Ta Wanke Tsohon Gwamnan Jigawa, Saminu Turaki Kan Zargin Almundahanar Biliyan 8.3
Mutanen kauyen sun kuma ce an kai wasu da dama da suka jikkata zuwa asibiti domin basu agaji.
Wani mai ba da shawara kan harkokin tsaro a karamar hukumar Guma, Waku Christopher, ya tabbatar da harin da aka kai wa mutanen karkarar.
Ya ce maharan dauke da makamai sun kama mutane biyar da ke aiki a gonakinsu tare da kashe su.
Christopher ya ce wasu mutane hudu da abin ya rutsa da su sun samu raunuka daban-daban.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Benuwe, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar harin amma har yanzu ba ta bada cikakken bayani kan faruwar lamarin ba.
“An tabbatar da kai harin a unguwar Yelwata. Jami’an ‘yansandan da aka tura yankin na ci gaba da gudanar da bincike. Za a bayyana cikakken bayanai da zarar an kammala bincike,” in ji kakakin.