Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Dutse a Jihar Jigawa ta sallami Sanata Ibrahim Saminu Turaki tare da wanke shi daga zargin almundahanar da ta kai Naira biliyan 8.3 da Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ke masa.
Turaki, tsohon gwamnan Jihar Jigawa da Kamfanoni 3 ne ake shari’a tun ranar 4 ga Mayu, 2007.
- Gwamnatin Kano Ta Yi Allah-Wadai Da Hare-Hare Da Kwacen Wayoyi Da Magoya Bayan NNPP Ke Yi
- ‘Yan Bindiga Sun Harbe Wani Mutum Lokacin Da Suka Kai Hari Yankin Maitama Da Ke Abuja
Hukumar EFCC ta gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu kan tuhume-tuhume 33 da suka shafi karkatar da kudaden jihar.
Alkalin kotun, mai shari’a Hassan Dikko, wanda ya yanke hukuncin, ya yi watsi da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa, ya kuma sallami duk wadanda ake tuhumar saboda rashin gamsassun hujojji.
Kotun ta kuma bayar da umarnin a ba shi takardun tafiye-tafiyensa wanda aka kwace.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, Saidu Muhammad Tudunwada daya daga cikin lauyoyin Saminu Turaki mai bayar da shawara kan tsaro, ya ce kotun ta samu cancanta cikin karar da suka shigar na sallamar wanda ake tuhuma kan laifuka 33.
Ya kara da cewa da hukuncin an yi adalci kuma nasara ce ga kowa da kowa.