• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yi Wa Sama Da Mutum 130 Gwajin Cutar Hanta Kyauta A Kano

by Khalid Idris Doya
3 years ago
Cutar Hanta

Cibiyar lafiya ta MGK Healthcare ta gudanar da taron wayar da kan al’umma tare da yi musu gwajin cutar hanta kyauta a jihar Kano inda mutu sama da 130 suka amfana.

Babban Jami’in gudanarwa na MGK Healthcare, Pharm. Isma’il Usman wanda ya wakilci babban shugaban asibitin, Muhammad Garba, ya shaidawa manema labarai jimkadan bayan kammala aikin da ya gudana a karshen mako a harabar asibitin a Kano, ya ce sun shirya wannan taron ne domin wayar da kan al’umma kan cutar ta hanta tare da karfafa su akan muhimmancin yin gwajin cutar domin samun kariya daga kamuwa da cutar tare da sanin maganin cutar tare da kuma yi musu gwajin cutar a kyauta.

  • Yau Alhamis Za A Yanke Hukunci Kan Malamin Da Ake Zargi Da Yi Wa Dalibarsa Kisan Gilla A Kano

Ya ce: “Domin mu tuna ranar Hanta ta duniya. Ranar hanta ta duniya ana tunawa da shi ne a ranar 28 ga watan Yulin kowacce shekara. Sannan a kowacce shekara akwai take da hukumar lafiya ta duniya take fitarwa na abin da za a maida hankali a kan shi. A wannan shekarar hukumar lafiya ta duniya ta fitar da sabon take na ‘kusanto da karfafa gwaji da kuma samar da magani ga mutane’”, ya lurantar.

Ya ci gaba da cewa; “Mun kalli wannan wani abu ne da za mu bayar da gudummawa wajen samar da lafiyar al’umma domin ganin cewar an kiyaye mutane daga kamuwa daga wannan cutar. Wanda suke da ita kuma a yi kokarin gano ta a kuma samar musu da hanyar da za su iya samun magani da shawarwari”.

Cutar Hanta

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

Da ya juyo dangane da shawarwarin da suke bai wa al’umma kan wannan cutar kuwa, Pharm Isma’il ya ce; “Cutar hanta cuta ce wacce mutane da dama su na dauke da ita ba tare da sun sani ba. Wasu da dama su na yawo da ita ba su san ma suna dauke da ita ba. Kididdiga ta nuna cewar akalla duk dakika 30 ana samun mutum daya da yake mutuwa a dalilin cutar da ke da alaka da cutar hanta”, ya nusasshe.

“Shawararmu ga al’umma shi ne su farga su kuma yi kokarin zuwa asibitoci domin a tantance su a tabbatar musu ko suna da wannan cuta ko ba su da shi.”

Ya yi takaitaccen bayani dangane da rabe-raben cutar hanta da yadda ake kamuwa da ita. Tare da zayyano irin aikin da hanta take yi a jikin dan Adam. “Hanta ita ke sarrafa abincin da muke ci da sha na yau da kullum, ta maida su yadda za su yi aiki sannan ta gabatar da su ga jiki. Wadansu abubuwan da za su iya illata jikin mutum ita ke canza su ta maida su yadda ba zai illata jikin ba,” ya lurantar.

Cutar Hanta

Ya nuna illar dake cikin a ce hantar mutum ta kamu da ciwo, inda ya ce; “daga lokacin da hanta ta illatu, zai zama dukkanin bangarorin jikin mutum zai zamo cikin illa.”

A karshe ya yi bayani dangane da ayyukan asibitin na MGK Healthcare, inda ya ce asibiti ne na kwararru da yake yin ayyuka daban-daban. Kuma suna da kananu da manyan likitoci da suke duba marasa lafiya daban-daban wadanda suka hada da masu zuwa a duba su su koma gida, da ma wadanda ake kwantar da su har sai sun samu lafiya.

Sannan ya ce daga cikin ayyukansu suna da bangaren masu kula da ciwon hakori, bangaren bayar da magunguna, bangaren gwaje-gwajen cututtuka manya da kanana, bangaren da ke haska cututtukan dake jikin mutum, sannan suna yin tiyatar da ya hada da na kashi, karbar haihuwa, na cututtuka, na kwakwalwa da jijiya da kuma na zuciya da sauran su.

“Sannan muna dauko marasa lafiyar da suke da bukatar taimakon gaggawa zuwa asibiti da motar daukar marasa lafiya wanda ake tafiya da ma’aikatan asibitin a cikinta. Sannan muna da gidauniyyar da take bai wa al’umma marasa karfi gudummawa a bangaren ilimi, kiwon lafiya da kuma muhalli”.

Har wala yau ya ce suna da lasisi a bangaren inshorar lafiya da gwamnatin Tarayya da ta jihar Kano da ma kamfanoni, wadanda ma’aikatan dake karkashin wadannan ke zuwa asibitin ana kula da lafiyarsu musamman wadanda suke karkashin inshorar lafiya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisa Na Binciken Kwangilar Titin Naira Biliyan 1.46 Da Aka Yi Watsi Da Shi A Kaduna
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

November 8, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu!
Rahotonni

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Next Post
Malaman KASU Sun Janye Yajin Aiki Bayan Barazanar El-Rufa’i 

Malaman KASU Sun Janye Yajin Aiki Bayan Barazanar El-Rufa’i 

LABARAI MASU NASABA

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Triumph

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.