Wasu da ba a san ko su waye ba sun yi wa wata yarinya ‘yar shekara 18 mai suna Miss Wassa Joel Tuwa ‘yar Karamar Hukumar Yoro ta jihar Taraba fyade har lahira a hanyar wani daji da ke kauyen Rankabiri kusa da Jalingo babban birnin Jihar Taraba.
Wata majiyar daga dangin wacca abin ya shafa, Mista Ayuba Solomon Bissa ya shaida wa wakilinmu cewa an yi wa Mis Tuwa fyade tare da kashe ta yayin da aka jefa gawar a bayan wani dutse kusa da Jalingo.
- Wasu Hukumomin Kasar Sin Sun Ware Miliyoyin Kudi Domin Tallafawa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa
- Rikicin Nijar: Tinubu Ya Aika Janar Abdulsalami, Sultan Na Sokoto Zuwa Yamai
A cewar Ayuba, marigayiyar ta bar gidansu da ke Jalingo zuwa Lankabirir, wani kauye kusa da yammacin ranar Asabar. Ta bi ta wata karamar hanyar kasuwa da ke kusa da Lankabiri don ta samu saukin tafiyar inda a nan ne suka tare suka yi mata fyade har ta mutu.
Ya kuma bayyana cewa binciken da likitocin suka gudanar ya nuna cewa an yi wa matar fyaden ne kafin daga bisani a kashe ta.
“A ranar Lahadi da safe ne wani karamin yaro da ke tallan itace ya gano gawar ta a gefen hanya, ya koma a guje ya sanar da iyayensa abin da ya gani, sai iyayen yaron da sauran mazauna wurin suka je wurin, suka gano gawarta a gefen hanya kusa da wani dutse.
“Ba mu taba gawarta ba, amma dai mun gayyaci jami’an tsaro da ke aiki a yankin domin su gani da kuma ba da shawara kan abin da za a yi, jami’an tsaron da suka hada da sojoji da ’yan sanda sun zo suka ba mu shawarar da mu kai gawar zuwa dakin ajiyar gawarwaki, mu ba da damar yin bincike.
“Mun kai gawar zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya Jalingo bayan likitan da likita ya kammala gudanar da bincike ya tabbatar mana da cewa an yi mata fyade ne kafin a daga baya a kashe ta.
“Ina so in yi kira ga jami’an tsaro da su zurfafa bincike domin a gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya,” in ji Ayuba.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba, PPRO Usman Abubakar, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu cikakken bayani kan lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp