Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Nijeriya (NPC), ta sanar da cewa ta yi wa yara sama da miliyan 10 rijistar haihuwa cikin watanni uku da suka gabata.
Wannan ci gaba ya nuna yadda ake karɓar shirin rijistar haihuwa a ƙasar, wadda ita ce mafi yawan jama’a a Afrika.
- NLC Ta Buƙaci Gwamnatin Tinubu Ta Soke Sabuwar Dokar Haraji
- 2025: Tinubu Ya Yi Alƙawarin Sauƙaƙa Tsadar Kayan Abinci Da Magunguna
Shugaban hukumar, Alhaji Nasir Isa Kwara, ya bayyana wannan alƙaluma yayin wani taron manema labarai da aka gudanar bayan ziyarar mai ɗakin shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, wadda ta karrama jaririn farko da aka haifa a shekarar 2025 a asibitin Asokoro, a Abuja.
Shugaban ya ce an samu karɓuwar rijistar haihuwa sosai a sassan Nijeriya.
Da yake wakiltar shugaban hukumar, kwamishinan ayyuka na Jihar Katsina, Bala Banya, ya ce NPC na aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa duk wani jariri an yi masa rijista a ko ina yake a Nijeriya.
Ya ƙara da cewa haɗin gwiwar da aka yi da asibitocin kula da lafiya a matakin farko da kuma amfani da sabon tsarin zamani ya taimaka sosai wajen samun wannan ci gaba.
A cewar Bala Banya, rijistar da aka yi ta haɗa da sabbin haihuwa da kuma yara ƙanana ‘yan ƙasa da shekaru biyar waɗanda ba a yi musu rijista a lokacin haihuwarsu ba.
Ya ce yanzu NPC ta fi mayar da hankali kan waɗannan yara domin cike giɓin rijistar.
A baya, babban daraktan hukumar, Dokts Telson Osifo Ojogun, ya sanar da cewa an shirya kafa cibiyoyin rijistar jarirai sama da 4,000 a faɗin ƙasar don sauƙaƙa aikin rijistar haihuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp