Zanga-zangar nuna goyon baya ga masu nuna kin amincewa ga samamen da gwamnatin Trump ke yi kan bakin haure na kara samun karbuwa a wasu biranen Amurka.
A New York, inda mutum 2,000 suka yi zanga-zanga, ‘yansanda sun kama mutane da dama da suka toshe hanya yayin da a Chicago aka kara kama wasu.
- Wakilin Sin: Matakin Amurka Game Da Harajin Kwastam Bai Yi La’akari Da Rarar Cinikayyar Hidimomi Ba
- Wutar Lantarki Mai Ƙarfi Ta Yi Ajalin Mutum Biyar A Gombe
Tun da farko wani alkali a Amurka ya ki amincewa da bukatar gaggawa daga gwamnan California ta hana amfani da dakarun tsaron da aka tura Los Angeles domin dakile zanga-zangar.
Wakilin BBC ya ce tura sojojin kundumbalar da Trump ya yi ne ya fusata mutane da dama har da gwamnan.
Mista Trump ya ce aike sojojin kundumbala da dakarun tsaro zuwa birnin ya zama dole domin hana abokan gaba samun galaba a Los Angeles.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp