Samar da tashar teku ta Baro da Gidauniyar (PTF) ta fara a shekarar 1995 ta kunshi bangarori da dama wadanda suka hada da samar da tsarin sufuri na zamani da kuma yashe kogin Neja don samar da isasshen ruwan da jiragen ruwa za su iya zirga-zirga a kai.
A kan wannan tsarin ne gwamnatin Marigayi Shugaban Kasa Umaru Musa Yar’Adua ta fara aikin yashe kogin da nufin samar da tasha ta zamani da za ta yi kafada da kafada da takwarorinta na sassan duniya.
- Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ya Amsa Tambaya Game Da Taron Ministocin Muhalli Da Yanayi Na G20
- Nuna Bambanci A Fannin Ba Da Ilmi Na Lahanta Makomar Amurka
Aikin ya fuskanci matsaloli da dama, musamman abin da ya shafi siyasa a zamanin tsohon Shugaba Jonathan, har sai da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zo da nufin ci gaba da aikin inda har ya kaddamar bangaren gudanarwa na tashar da sashen ajiye kayayyaki.
A ranar 19 ga watan Janairu 2019 aka yi gaggarumin bikin kaddamar da aikin tashar, inda al’umma da dama suka yi fatan hakan zai farfado da harkokin tattalin arzikin yankin Arewa da ma Nijeriya gaba daya.
Amma sai gashi wannan fata na al’ummun da ke kewaye da garin na Baro ya dushe, shekara hudu ke nan da aka kaddamar da aikin lokacin da Buhari yake neman a sake zabensa a wa’adi na biyu.
A shekarar 2019 jam’iyyun adawa sun nuna rashin gamsuwarsu a kan yadda aka yi gaggawar kaddamar da tashar suna masu alakanta hakan a kan cewa, siyasa ce kawai ba da gaske ake yi ba, musamman ganin yadda aka faro akin kamar da gaske.
Haka kuma a shekarar 2020, shekara daya bayan kaddamarwar, wasu kungiyoyin masu fafutukar ganin an ci gaba da aikin tashar, sun nuna damuwa da rashin amincewarsu a kan yadda aka kasa ci gaba da aikin ko da samar da kayan da ake bukata ne a adana.
Kungiyar da ke fafutukar ceto aikin tashar ta Baro mai suna ‘Baro Port Rescue (BPR)’ wadda ke samun goyon bayan wata kungiya a kan cimma nasarar harkokin da suka shafi teku ‘The Blue Resolution Initiatibe (TBRI)’, a tattaunawar da suka yi da manema labarai, ta hannun Babban sakataren kungiyar, Ibrahim Ja’afar ta bayyana cewa, sun ziyarci tashar inda suka fahimci cewa, tashar ba ta kai matakin da za ta iya aikin da akenufa ba.
Ya kara da cewa, bayan ziyarar da kungiyoyi masu zaman kansu 24 suka yi a tashar sun tabbatar da cewa, tashar ta Baro na cikn mawuyacin hali, kuma tuni aka yi watsi da aikin gaba daya.
Kungiyar ta bayyana cewa, da kyar in har an kammala akalla kashi 30 zuwa 40 na aikin, ko kusa ba a kammala yashe kogin ba.
Jafa’aru ya kara da cewa, lallai an biya diyya yadda ya kamata ga al’ummun da aikin tashar ya shafa amma kuma har zuwa yanzu al’ummun ba su ga amfanin tashar ba saboda yadda gwamnati ta yi watsi da aikin.
Bincike ya nuna cewa, a shekarar 2020, wasu masu ruwa da tsaki a jihar, musamman wadanda suka fito daga yankin Neja ta Kudu sun yi wani gaggarumin taro a garin na Baro wanda aka tabbatar da cewa, gari ne na kasuwanci mai dadadden tarihi don su jawo hankalin gwamanatin tarayya a kan bukatar a kammala aikin ba tare da bata lokaci ba.
Sanata mai wakiltar yankin Neja ta Kudu a lokacin, Mohammed Bima Enagi ya ce, cikin manyan abubuwan da ake bukata don tashar ta fara cikakken aiki ya hada da yashe kogin Neja tun daga Warri zuwa Jebba.
Ya kuma kara da cewa, ba za a kai ga cin gajiyar tashar ba in ba an gyara dukkan hanyoyin da suka kai ga garin na Baro ba, musamman ganin a halin yanzu duk sun lallace, “Dole a gyara hanyoyin in har da gaske ake yi” in ji shi.
Ya ce, wasu abubuwan da ake bukata in ana so a samu nasarar samar da tashar Baro su ne gina hanyar jirgin kasa ta zamani, hakan zai farfado da harkokin tattalin arziki na yankin gaba daya, musamaman abin da ya shafi harkokin noma da na ma’adanai.
A kan haka na bukaci gwamnatin tarayya ta samar da kudaden da ake bukata don kammala akin musamman ganin muhimmancin aikin ga rayuwa al’ummar jihar Neja da ma Nijeriya gaba daya.
Wannan na zuwa ne shekara 4 bayan kaddamar da aikin, inda suka nuna damuwarsu suna masu cewa, daga dukkan alamu barin aikin babbar asarar kudaden al’umma ne da aka riga aka narkar, kuma hakan ya gaskata bayanan da jam’iyyun adawa suka yi tun a farkon shirin ya kuma tabbatar da tsoron da masu ruwa da tsaki suka nuna a kan cewar aikin yaudarar al’umma ne aka yi don cimma manufar siyasa.
LEADERSHIP Hausa ta lura da yadda ciyayi da shuke-shuke suka mamaye tashar da aka kashe biliyoyin kudi don samarwa, ga kuma yadda ruwa yake neman kassara gabar kogin, abin da ke barazana ga gine-ginen da aka yi.
Bincike ya nuna cewa, bangaren farko da aka kaddamar a shekarar 2019 ya lakume fiye da Naira Biliyan 3.5, wannan kuma ba a sa kudaden yashe kogin ba a lokacin da aka kaddamar da aikin.
Al’ummar Baro sun bayyana cewa, ba kamar yadda gwamnatin tarayya ta bayyana ba, ba ta da niyyar tashar ta fara aiki nan take bayan kaddamarwar da aka yi tun da farko.
Wani Injiniya da ke aiki a tashar da ya nemi mu sakaya sunansa ya bayyana wa LEADERSHIP Hausa cewa, “An tsara tashar Baro ce ta yadda za ta rika karbar manyan kwantainan kayyaki ta hanyar kananan jiragen ruwa daga Legas ta Lakwaja har zuwa Baro ta hanyar amfani da kogin Neja, amma a yau tashar da aka kaddamar tana nan duk ciyayi sun mamaye.”
Ya kara da cewa, duk da an kaddamar da tashar ne ba tare da samar da abubuwan da za su taimaka wajen ganin ta fara aiki yadda ya kamata ba amma duk da haka da za a ci gajiyar tashar matukar an mayar da hankali wajen samar da ingantattun hanyoyi mota da layin jirgin kasa da suka nufi tashar.
Masanin ya kuma kara da cewa, baya ga kayan aikin da ba a kai ga samarwa ba, ba za a samu shigowar manyan kayayyaki daga kasashen waje ba musamman saboda gadar nan ta Murtala da ke Jamata da sauran gadajojin da ke kan hanyar da taso daga Warri ba su da inganci.
Haka kuma Sarkin Baro, Alhaji Salihu Ndanusa ya nuna rashin jin dadinsa a kan halin da hanyoyin da ke yankin suke ciki tun bayan da aka kaddamar da aikin shekara 4 da suka wuce, ba a samu gyara hanyoyin da suka taso daga Katcha, Agaie, da Gulu zuwa Abuja ba har yanzu, inda ya ce wannan yana kange tashar daga shigowar mutane.
Wani shugaban matasa da ya taba zama mamba a majalisar dokokin jihar Neja, Hon Jibrin Akwanu, ya ce, “An damfare mu ne aka kaddamar da aikin shekara 4 da suka wuce saboda siyasa, a lokacin da suke yakin neman zabe, bayan sun ci zabe kuma suka yi watsi da aikin.”
A ta bakin wani dan asalin yankin, Nuhu Ibrahim ya ce, “Rashin ci gaba da aikin ya kawo mana cikas sosai, yawancin matasan kauyukan da ke yankin da su aka yi aikin gina tashar kuma sun samu rufin asiri, mun kuma sa ran za mu ci gaba da amfana da ayyukan tashar sai gashi aiki ya tsaya cak. Muna kira ga gwmanatin tarayya da duk wanda yake da hannu a ganin an ci gaba da aikin ya taimaka don muna tsananin bukatar dawowar aikin.
“Ci gaba da aikin na daya daga cikin hanyoyin da Shugaban Kasa Bola Ahed Tinubu zai saka wa yankin Arewa ta tsakiya, musamman ganin irin goyon bayan da muka bashi a lokacin zaben 2023.” In ji shi.