Mazauna Bauchi, Gombe, da Dutse sun bayyana damuwarsu kan zargin karkatar da tallafin shinkafar Gwamnatin Tarayya da ake nufi don rage wa mutane raɗaɗin tsadar rayuwa.
Gwamnatin ta ware tireloli 20 na shinkafa ga jihohi 36 tare da sauran kayan agaji a matsayin tallafi ga marasa galihu saboda ƙalubalen tattalin arziƙin da ake fuskanta. Amma mutane a waɗannan jihohi suna zargin cewa an karkatar da rarraba kayan zuwa wani wajen daban.
- Shin Barcelona Da Atletico Madrid Zu Su Iya Dakatar Da Real Madrid A La Liga?
- Shugaba Tinubu Ya Yi Alhinin Rasuwar Sarkin Ningi
A Dutse, Jihar Jigawa, suna zargin jami’an gwamnati da fifita magoya bayan jam’iyyarsu wajen rabon tallafin. Alhaji Muhammadu Hamza ya soki yadda aka gudanar da rabon, inda ya ce iyalai da dama masu buƙata basu samu komai ba.
Haka zalika, Malam Musa Ali da Hajiya Maimuna sun zargi jami’ai da damfarar talakawa daga samun tallafin da ya dace da su.
A Bauchi, jinkirin rarraba shinkafar ya tada hankalin mazauna da ke jin tsoron ko an boye tallafin. Malam Sani Muazu ya ce jinkirin ya kara tsananta matsalar abinci ga talakawa. Shugaban ƙungiyar hada kan ƙungiyoyin Jama’a na Bauchi (BASNEC), Garba Jinjiri, ya bayyana irin wannan damuwa tare da bayyana rashin jin daɗin cire ƙungiyoyin jama’a daga kwamitin rabon kayan.
Wani babban jami’in Ma’aikatar Harkokin jin Kai ta Jihar Bauchi, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce har yanzu jihar ba ta samu tallafin ba, amma ya tabbatar da cewa idan an samu za a rarraba kai tsaye.
A Gombe, mazauna irinsu Mrs. Audu Alheri da Musa Ahmed sun yi ikirarin cewa ba a raba tallafin shinkafar gwamnatin tarayya ba, inda wasu ke zaton an boye kayan.
Shugaban Gombe Network of Civil Society (GONET), Yusuf Ibrahim, ya yaba da kokarin gwamnatin jihar, amma ya nemi inganta gaskiya a tsarin.
Yayin da wannan ce-ce-ku-ce ke ci gaba da faruwa, mutane suna kira ga gwamnatocin jihohin da su tabbatar tallafin ya kai ga waɗanda suka fi buƙata, tare da gudanar da tsarin rarraba tallafin cikin gaskiya da adalci.