• English
  • Business News
Sunday, June 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ana Fargabar Boko Haram Ta Kara Mamaye Wasu Kananan Hukumomi A Borno

by Muhammad Maitela
3 weeks ago
in Rahotonni
0
Ana Fargabar Boko Haram Ta Kara Mamaye Wasu Kananan Hukumomi A Borno
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A daidai lokacin da al’ummar Nijeriya suke murnar bankwana da hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram da ISWAP, a Arewa Masu Gabas, musamman jihohin Borno da Yobe, hadi da wasu yankuna, sai gashi an raka bako ashe ya make a bayan gari.

Wannan yana zuwa ne sakamakon yadda kungiyar take aiwatar da sabbin hare-haren ta’addanci a wurare daban-daban.

  • Darajar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso Shida Bisa Dari A Afirilu
  • Tsaro Ya Inganta A Zamfara, In Ji Gwamna Lawal Yayin Tattakin Zaman Lafiya Na Tarihi A Jihar

Sabbin hare-haren sun fara aiwatar da su a sansanonin sojojin Nijeriya, wadanda suke ayyukan samar da tsaro a yankin, tare da kai wasu farmakin a garuruwa daban-daban, al’amarin da ya jawo asarar rayukan jami’an da dama kana kuma haifar da koma-bayan tsaro, idan an kwatamtata da ci gaban da ake samu a cikin ‘yan shekarun da suka gabata.

Baya ga aiwatar da hare-haren, abin bai tsaya nan ba, sun hada da garkuwa da jama’a da dasa nakiyoyi kan hanyoyi da saka bama-bamai a muhimman wurare, wanda hakan babbar barazana ce a sa’ilin da gwamnati ke ikirarin kawo karshen matsalar tsaron, kuma akwai bukatar a yi wa tufkar hanci wajen dakile yaduwar ayyukan ta’addanci a kasa baki daya.

A kwanan baya, Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Garbai El-Kanemi, bayan ya yaba wa kokarin hukumomin tsaro a yaki da ayyukan ta’addanci, haka kuma ya jaddada bukatar daukar kwararan matakan dakile yaduwar ayyukan ta’addanci, inda ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba, saboda har yanzu akwai kananan hukumomi uku; Guzamala, Marte, da Abadam da wasu sassan Mobbar, suna karkashin ikon Boko Haram.

Labarai Masu Nasaba

Sarkakiyar Da Ke Tattare Da Zaben 2027 Da Yadda Za Ta Kaya

2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

A wancan lokacin, sojojin Nijeriya sun musanta batun Shehun Borno, amma wasu na ganin cewa akwai kashan gaskiya dangane da wannan al’amari, sakamakon irin yadda ‘yan ta’addan ke cin karensu babu babbaka a wadannan yankuna.

Shi ma a nasa bangaren, mai sharhi kan kungiyoyin ta’addanci a Cibiyar Tony Blair, Barista Bulama Bukarti, ya ce, “A binciken da muke da shi, mun gano yadda Boko Haram suke amfani da jirage marasa matuka wajen kai wasu hare-hare a sansanonin sojojin Nijeriya.”

Idan an yi la’akari da wadannan bayanan sun nuna cewa kungiyar Boko Haram tana ci gaba da fadada ayyukanta a fannoni daban-daban ba tare da an taka mata birki ba.

Bisa ga wannan ne, Sanata Mohammad Ali Ndume, mai wakiltar kudancin Jihar Borno, ya ce dawowar hare-haren Boko Haram babban abin takaici ne wanda bai kamata gwamnati ta yi sakaci dangane da wadannan sabbin hare-haren da kungiyar take aiwatarwa a wasu yankunan jihar ba, musamman a sansanonin sojojin Nijeriya.

Duk da wasu shirye-shirye na dakile lamarin, Boko Haram ba ta daina aiwatar da munanan hare-hare kan sojoji da fararen hula ba. Saboda ko a cikin watan Maris na 2025, Boko Haram da ISWAP sun kai hari wani sansanin soja a Borno, inda suka kashe sojoji hudu tare da lalata makaman yaki, kamar yadda Kamfanin Reuters ya ruwaito. Sannan sun kai karin wani hari a sansanin rundunar hadin gwiwa ta MJTF da ke Wulgo, inda suka kashe sojoji 12 suka jikkata wasu goma sha biyu.

Abin bai tsaya nan ba, inda a ranar 12 ga watan Janairun da ya gabata, kungiyar ta kashe manoma 40 a Dumba kusa da Baga da ke Jihar Borno. Sannan kuma a ranar 12 ga watan Afrilun wannan shekara, a wani harin bam da kungiyar ta dasa a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, ya kashe fararen hula takwas tare da jikkata karin wasu 21.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya bayyana fargabar cewa saura kiris karamar hukumar Marte, mai kimanin garuruwa 300 ya koma hannun ‘yan ta’adda, inda zancen da ake yi yanzu, gari daya ne kawai ya rage, wanda mayakan Boko Haram ba su mamaye ba, ya yi gargadin cewa bai kamata a bari ta fadawa a hannun ‘yan ta’adda ba.

Gwamnan ya yi wannan kan-da-garkin a ranar Lahadin da ta gabata, sa’ilin da ya kai wata ziyara a yankin, inda ya roki gwamnatin tarayya da ta yi amfani da dukkan matakan da suka dace cikin gaggawa wajen dakile yunkurin Boko Haram da ISWAP na kwace Marte.

A wannan ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a Marte, domin gani da ido dangane da halin da ake ciki a yankin tare da kokarin lalabo mafitar zaman lafiya mai dorewa. A tattaunawarsa da manema labarai, gwamnan ya ce ziyarar ta zo ne don karfafa gwiwar al’ummar yankin, su samu juriya, da ci gaba da hadin kai tare da tallafa wa kokarin hukumomin tsaro.

Zulum ya kara da cewa, sakamakon matsalolin tsaro da yawan kai hare-hare ba kakkautawa a baya, hakan ya tilasta zakuda garin Marte; shekaru hudu da suka wuce, amma abin takaici, kwanaki uku da suka gabata, Boko Haram sun sake barnata gayin, al’amarin da ya jawo jama’a sake yin gudun hijira.

Ya ce, “Kimanin mutum 20,000 sun bar Marte zuwa Dikwa; wannan adadin babbar barazana ce, saboda zaman wannan adadi a sansanonin gudun hijira, akwai fargabar yawancin matasa su karkata zuwa shiga kungiyoyin ‘yan ta’adda.

“Wannan karamar hukumar Marte ta kunshi garuruwa da kauyuka sama da 300, amma yanzu gari daya kacal ya rage. Kuma muddin muka yi sakaci, ko shakka babu Marte zai fada hannun ‘yan ta’addan, wannan abin tsoro ne, kuma ina kyautata zaton hakan ba zai kasance ba.

“Saboda haka, ina kira ga gwamnatin tarayya tare da sojojin Nijeriya, mu hada kai wajen hana yuwuwar faduwar Marte zuwa ga kungiyar Boko Haram,” In ji Zulum.

Zulum ya nuna karfin gwiwarsa da cewa, mafi yawan ‘yan gudun hijira sun fara komawa bayan wannan ziyarar da ya kai tare da yaba da kokarin hukumomin tsaro da masu aikin sa-kai.

“Alhamdulillah, mun shiga garin Marte jiya kuma mun kwana tare da taimakon sojojin Nijeriya da masu aikin sa-kai, kuma al’umma sun zauna karo na biyu. Duk da haka, addu’ar da nake yi, Allah ya sa gwamnatin tarayya da sojojin Nijeriya su yi duk abin da za su iya don kiyaye wannan garin,” in ji shi.

Har ila yau kuma, gwamnan ya sake jaddada aniyarsa na tallafa wa sojojin Nijeriya a kokarinsu na dawo da zaman lafiya a fadin Jihar Borno.

Gwamna Zulum, ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa da jami’an sojojin Nijeriya suna da hannu wajen rura wutar matsalolin tsaro, ta hanyar bai wa ‘yan ta’adda bayanan sirri tare da hadin gwiwa da ‘yan ta’addan Boko Haram.

“Wadannan ‘yan ta’adda suna da masu ba su bayanan sirri tare da hadin gwiwa a cikin sojojin Nijeriya, da kuma cikin ‘yan siyasa, da kuma cikin al’umma. Saboda haka, babban abin da za mu yi shi ne, dole mu karfafa hanyoyin samar da bayanan sirri na leken asiri don dakile wadannan matsaloli.”

Gwamnan ya sake jaddada cewa akwai bukatar Nijeriya ta samar da sabbin dabarun yaki da ta’addanci domin samun dawamamen zaman lafiya, tare da dakile hanyoyin ta’addanci.

A wani rahoton da BBC Hausa ta fitar, baya ga karamar hukumar Marte, akwai karin wasu kananan hukumomi wadanda suke fuskantar barazanar Boko Haram a Jihar Borno, wadanda suka hada da Bama, wanda a tattaunawar, Dakta Kabir ya bayyana Bama a matsayin wuri mafi tsanani samun hare-haren Boko Haram suka tagayyara a jihar.

Sauran sun hada da karamar hukumar Konduga, gari ne wanda yana daya daga cikin wuraren da hare-haren Boko Haram suka yi kamari. Sai Gwoza, Dikwa, Askira-Uba, Damboa, Mafa da Jere duk a Jihar Borno.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa kimanin manoma 50 ne ake zargin mayakan Boko Haram sun kashe ta hanyar yi musu yankan rago, a kauyen Malam Karanti, da ke karamar hukumar Kukawa a Jihar Borno.

Wadannan manoman sun kasance a karkashin kulawar daya daga cikin kwamandojin kungiyar ISWAP, wanda ake kira Amir Akilu, wanda aka ce shi ne yake kula da kauyukan Malam Karanti zuwa Dawashi, wanda suke bai wa manoma da masunta tsaro, su kuma suna biyan haraji akai-akai ga kungiyar ‘yan ta’addan.

Wata majiyar ta bayyana cewa kungiyar ISWAP sun kai harin ne sakamakon zargin manoman da yi musu leken asiri zuwa ga jami’an tsaro.

Daya daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya a harin, ya ce ‘yan ta’addan sun kewaye manoman tare da yi musu barazanar kasa duk wanda ya yi kokarin gudu.

“Wasu daga cikinmu sun fara roron wake sa’ilin da suka kai mana wannan hari. Sannan kuma suka tattara mu, suka bayyana mana cewa za su harbe duk wanda ya yi kokarin gudu. Sun yanka mutane da yawa, na ga wadanda aka yi wa yankan rago da idona. Amma na zabi na gudu maimakon in jira a yanka ni.

“Sun kashe fiye da mutum 50, kuma mafi yawa an yi musu yankan rago. Haka kuma sun sace wasu” in ji shi.

Haka kuma Gwamna Zulum ya yi zargin cewa, sojojin Nijeriya ba su da isassun kayan aikin da suke bukata wajen tunkarar ‘yan ta’addan Boko Haram.

Gwamnan ya bayyana hakan a wata hira da ya gudanar da manema labarai, ya ce ‘yan ta’addan a halin yanzu suna amfani da fasahar zamani wajen aiwatar da hare-haren ta’addanci.

Zulum ya bukaci Shugaba kasa Bola Tinubu ya saurari sojoji kan abubuwan da suke bukata don kawo karshen ta’addanci a arewacin kasar nan.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Borno
ShareTweetSendShare
Previous Post

Shugaba Tinubu Ya Aika Tawaga Zuwa Jihar Neja Kan Ambaliya Ruwa

Next Post

Tsohuwar Firaministar New Zealand: Ya Dace A Koyi Dabarun Sin Na Raya Kasa

Related

jam'iyyu
Rahotonni

Sarkakiyar Da Ke Tattare Da Zaben 2027 Da Yadda Za Ta Kaya

1 week ago
Borno
Rahotonni

2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

2 weeks ago
Tsadar Rayuwa: Yadda Al’umma Suka Yi Sallah Cikin Kunci
Rahotonni

Tsadar Rayuwa: Yadda Al’umma Suka Yi Sallah Cikin Kunci

2 weeks ago
Kokarin Minista Tuggar Na Mayar Da Hijirar Masana Daga Nijeriya Zuwa Kasashen Waje Alhairi
Rahotonni

Kokarin Minista Tuggar Na Mayar Da Hijirar Masana Daga Nijeriya Zuwa Kasashen Waje Alhairi

3 weeks ago
Faduwar Jarrabawar JAMB Ta Tayar Da Bukatar Neman Sake Fasalin Hukumar
Rahotonni

Faduwar Jarrabawar JAMB Ta Tayar Da Bukatar Neman Sake Fasalin Hukumar

4 weeks ago
Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi
Rahotonni

Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi

2 months ago
Next Post
Tsohuwar Firaministar New Zealand: Ya Dace A Koyi Dabarun Sin Na Raya Kasa

Tsohuwar Firaministar New Zealand: Ya Dace A Koyi Dabarun Sin Na Raya Kasa

LABARAI MASU NASABA

Kiran Gwamnatin Tarayya Ga ‘Yan Jarida: Ku Zama Jigo Wajen Gina Dimokuraɗiyyar Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya Ga ‘Yan Jarida: Ku Zama Jigo Wajen Gina Dimokuraɗiyyar Nijeriya

June 22, 2025
Matsalolin Rayuwa: Matasan Suleja Na Buƙatar Ƙarfafa Gwuiwa

Matsalolin Rayuwa: Matasan Suleja Na Buƙatar Ƙarfafa Gwuiwa

June 22, 2025
Babban Al’amari Ne A Samu Ƴar Shekara 6 Ta Haddace Qur’ani A Makarantar Raudatul Jannah – Mai Sikeli

Babban Al’amari Ne A Samu Ƴar Shekara 6 Ta Haddace Qur’ani A Makarantar Raudatul Jannah – Mai Sikeli

June 22, 2025
Liverpool Za Ta Kece Raini Da Bournemouth, Arsena Za Ta Bakunci Man Utd A Wasan Mako Na Firimiya Ta Baɗi

Liverpool Za Ta Kece Raini Da Bournemouth, Arsena Za Ta Bakunci Man Utd A Wasan Mako Na Firimiya Ta Baɗi

June 22, 2025
Batun Rushe Gidaje A Unguwar Rimin Zakara Ba Gaskiya Ba Ne – Alhaji Naziru 

Batun Rushe Gidaje A Unguwar Rimin Zakara Ba Gaskiya Ba Ne – Alhaji Naziru 

June 22, 2025
FIRS Ta Umarci A Rika Bude Ofishoshin Karbar Haraji A karshen Mako

FIRS Ta Umarci A Rika Bude Ofishoshin Karbar Haraji A karshen Mako

June 21, 2025
CMG Ya Ja Hankulan Baki A Dandalin Tattaunawar Tattalin Arziki Na Kasa Da Kasa Na St. Petersburg Karo Na 28 

CMG Ya Ja Hankulan Baki A Dandalin Tattaunawar Tattalin Arziki Na Kasa Da Kasa Na St. Petersburg Karo Na 28 

June 21, 2025
Yankin Taiwan Ya Yi Taron Bikin Bauta Na Kakan Gargajiyar Sin Fuxi

Yankin Taiwan Ya Yi Taron Bikin Bauta Na Kakan Gargajiyar Sin Fuxi

June 21, 2025
EFCC Ta Gurfanar Da Wasu Kamfanoni Biyu Gaban Kuliya Bisa Damfarar Naira Miliyan 80

EFCC Ta Gurfanar Da Wasu Kamfanoni Biyu Gaban Kuliya Bisa Damfarar Naira Miliyan 80

June 21, 2025
Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Da Rasha Don Daukaka Amincewar Juna Ta Fuskar Siyasa Da Karfafa Muradun Juna

Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Da Rasha Don Daukaka Amincewar Juna Ta Fuskar Siyasa Da Karfafa Muradun Juna

June 21, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.